An kashe matar Firai ministan Lesotho

Dama dai ana zaman doya da manja tsakanin ma'auratan Hakkin mallakar hoto China TV
Image caption Dama dai ana zaman doya da manja tsakanin ma'auratan

An kashe matar Firai ministan mai jiran gado na kasar Lesotho, Thomas Thabane 'yan kwanaki kafin a rantsar da shi.

Rahotanni sun ce an harbi Di-polelo Thabane ne lokacin tana tafiya cikin mota tare da kawarta a Maseru babban birnin kasar.

Dama dai ana zaman doya da manja ne tsakaninta da maigidanta, abin da ya sa ba sa zaune a gida daya.

Labarin mutuwar DipoleloThabane da ke da ban mamaki ya zo ne 'yan kwanaki kafin a ranstar da tsohon mijinta Thomas Thabane, karo na biyu a matsayin Firaministan ƙasar Lesotho.

Ma'auratan, wadanda ba sa tare a matsayin mata da miji tsawon shekaru, suna shirin rabuwa gabanin kisan, kuma Mr Thabane ya sake auren matarsa ta uku wadda ya ke fita da ita bainar jama'a a kai a kai.

Maƙwabta sun bayyana cewa a cikin wannan makon, sun ga wasu gungun maza na buga ƙofar gidan mai ɗakin Firai ministan.

Kwana biyu bayan haka aka harbe ta.

Ba a sani ba ko wannan kisa na ranar Laraba na da alaƙa da siyasa, saboda har yanzu Mr Thabane na da maƙiya a cikin sojoji bayan yunƙurin juyin mulkin da ya jagoranta a shekarar 2014 - ko kuwa kisan na da nasaba da rashin jituwa tsakaninsu.

Alamu na nuna cewa Dipolelo Thabane ta yi nasara a babbar kotun a shari'ar da suke da mijinta, inda kotu ta bata ikon zama uwargidan Firai ministan, ko da yake yana zaune tare da matarsa ta uku.

Ana sa ran za'a rantsar da Mr Thabane a matsayin Firai ministan ƙasar karo na biyu cikin shekara biyar a ranar Juma'a.

Labarai masu alaka