ADIKON ZAMANI: Wacce matsala 'yar-aiki ke fuskanta?

Adikon Zamani

Ƙasidar wannan makon ta duba alfanun da ke tattare da dauko'yar aiki, da dalilan da iyaye kan bayar na tura yara mata kanana su yi aiki a birane, da illar da wannan al'ada ke haifarwa.

Filin ya tattauna da Hajiya Saudatu Mahdi, shugabar kungiyar WRAPA mai kare hakkin mata, da Malama Fa'iza, wata matar aure wacce ke daukar 'yar aiki, da kuma Malam Abdullahi, daya daga cikin mai kawo irin wadannan yara.

Shekarun Jamila takwas da haihuwa. An kawo ta Abuja daga kauyen Kura na jihar Kano domin ta yi aikin gida, saboda ta samu kudin sayan kayan daki idan lokacin aurenta ya yi.

Ta kan tashi da asubar fari ta shirya abincin da iyalin da take wa aiki za su karya da shi, sannan ta share gidan mai hawa uku daga kasa har sama.

Har ila yau, tana shirya yaran gidan gabanin tafiyarsu makaranta, kafin ta jira umarnin uwar dakinta.

Da rana, bayan uwar dakinta ta farka daga barci, ta kan yi ma ta dukkan hidimar da ta bukata ban da shirya abincin rana da take yi kafin dawowar yaran gidan daga makaranta.

Da yamma kuma za ta kama aiki tukuru na shirya abincin dare da gyaran gidan kafin mai gidan ya dawo.

Ba ta da hutu sai can cikin dare bayan uwar dakinta ta yi barci.

A wannan lokacin ne mai gidan ya kan kewayo ya ci zarafinta.

Ba ta iya cewa komai. Ba ta iya hutawa. Ba ta da ranakun hutu. Ba ta yin wasa, ta ji dadin rayuwarta kamar 'ya'yan gidan.

Tana nesa daga gidansu, kuma tana tuntubarsu ne kawai ta hanyar Hajiyar wadda ta kawo ta birnin.

Jamila na son shiga makaranta.

Labarin Jamila tamkar walkiya ce a damina.

Dukkan mu muna da alhaki. Mu kan 'shigo' da irin wadannan 'yan matan kauyen daga gidajensu saboda talauci, su yi ta mana aiki ba iyaka.

Muna muzguna masu matuka, amma suke kula da gidajenmu da 'ya'yanmu.

Kamar su ba mutane ne masu bukatar so da jagoranci ba.

Kusan ko wane gida ka shiga za ka taras da akwai a kalla 'yar aiki guda daya, wacce aikinta ne ta yi ayyukan da mu ba ma son yi.

'Yan aikin sun hada da yara kanana zuwa zawarawa.

A yau ina son yin tambaya: shin yaya kuke kula da 'yar aikinku?

Kuna kula da ita kamar 'yar uwarku, ko ko ta zama wacce dole a ke zaune da ita?

Kuna koya mata wani abu ko kuwa kun dauke ta ma'aikaciya ce (ko baiwa ce) kawai, wacce ke damun ku domin babu abin da ta iya?

Ko yaushe muna son kushe 'yan aikinmu, mu kan ce ba su da tsafta, ko ba su da natsuwa, amma mun taba yin wani yinkurin taimaka masu da zammar ci gabansu?

Yaya kuke ganin Jamila ke ji idan ta ga 'ya'yan uwargidanta sun tafi makaranta, amma ita tana gida tana bauta?

Wata kawata wacce yanzu lauya ce, kuma matar wani gwamna ce, - a da 'yar aiki ce a lokacin tana karama.

Ta yi sa'a gidan da take aiki sun tura ta makaranta, kuma duk da yawan ayyukan da take yi, tana da hazaka a makaranta.

Ta samu zuwa jami'a bayan da aka dauki nauyinta, kuma ta fita da da kyakykyawan sakamako a makarantar horar da lauyoyi.

Saboda ta na da ilimi, babu wata yarinya a gidansu da za ta zama 'yar aiki.

An yanke wa talauci kauna a gidansu, watakila har abada.

Shawarata ita ce, idan kuna da wata yarinyar da ke renon 'ya'yanku, kuma tana kula da gidajenku, ya kamata ku tallafa mata.

Ku duba yadda za ku iya taimaka ma rayuwarta, har sai ta fi yadda kuka same ta.

Na san wasu ba za su yarda da ni ba, amma dalili na shi ne: mu (da 'ya'yanmu) ba za mu samu kwanciyar hankalin more rayuwarmu ba, idan wani bangare na al'ummarmu na dakare a cikin talauci da jahilci.

A takaice, hakkinmu ne mu yi kokarin kawo cigaba ga al'ummarmu, ta fara taimaka wa yarinya daya, da almajiri daya a kai a kai.

Ga masu saurarenmu a rediyo akwai tattaunawa a kan batun da Hajiya Saudatu Mahadi, da Malama Fa'iza (sai ku latsa alamar lasifika da ke sama don ku saurara)

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Adikon Zamani: 'Yar aiki ko baiwa?