Nigeria ta nemi afuwar Saudiyya saboda sayar da dabinon sadaka

Najeriya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Saudi ta bawa Najeria kyautar dabino

Ma'aikatar harkokin kasashen waje ta Najeriya ta nemi afuwar kasar Saudiyya saboda wani abin takaici na sayar da dabinon da kasar ta ba Najeriya kyauta.

Gwamnatin Saudiyyar ta bayar da dabino tan 200 a matsayin wata kyauta ta azumin watan Ramadan, amma ma'aikatar ta gano wasu na sayar da dabinon a kasuwanni.

Ma'aikaytar ta gode wa kasar ta Saudiyya, sabili da karamcin da tayi, kuma ta sha alwashin gano wadanda suka aikata wannan laifin.

Sanarwar da kakakin ma'aikatar, Clement Aduku ya fitar ta ce, "Abin lura shi ne bayan da aka kammala rabon dabinon, ma'aikatar harkokin kasashen waje ba ta da sauran alhaki."

"Abin takaici ne a ce wasu na sayar da dabinon domin riba". inji Aduku

Ya kara da cewa "muna fatan ci gaba da aiki tare da kasar ta Saudiyya a fannonin daban-daban".