Gobarar Landan: Dabarar da 'yan kwana-kwana ke amfani da ita

Hoses are used on Grenfell Tower Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ginin na "Grenfell Tower" mai hawa 24 ya mamaye da hayaki

Yadda aka ga wuta ta kama gini mai hawa 24 a yammacin birnin Landan ya gizgiza Birtaniya.

'Yan kwana-kwana suna fama da kashe gobara a dogayen benayen manyan biranen duniya, ko akwai wani darasi da aka koya?

Wani tsohon jami'in kashe gobara Bob Parkins, ya ce 'yan kwana-kwana sukan fara da ajiye kayan aikinsu a hawa biyu kasa da ainihin inda gobara take .

Yawan lokacin da kowanne dan kwana-kwana zai yi yana kashe gabarar ya ta'allaka ne da yawan iskar da take samuwa.

Don haka mintunan da aka bata yayin hawa ginin lokaci ne mai matukar muhimmanci da ake batawa.

Mista Parkin ya ce "Za ka yi amfani da iska mai yawa yayin da kake hawa zuwa hawa na 10, saboda haka muke kafa sansaninmu kasa da inda gobarar take da hawa biyu".

"Idan suka samu damar shiga ciki, abu na farko da suke yi shi ne su kubutar da wadanda gobarar ta rutsa da su."

"Daga nan sai su fara kashe gobarar, saboda wannan dalilin ne 'yan kwana-kwanan ke daukan takaitattun kayan aiki," in ji shi.

"Dole su samu hanyar shiga cikin ginin a wasu lokuta, amma za su iya yin kasada idan rayukan jama'a na cikin hadari, shakka babu."

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An tabbatar da cewa katako ne ya haddasa bazuwar wutar Torch Tower ta Dubai a shekarar 2015

Har ila yau, Mista Parkin ya ce abin da ya faru da ginin "Grenfell Tower" a birnin Landan abu ne mai matukar wahala, saboda wutar ta bazu cikin sauri, kuma ta samu damar mamaye kusan ilahirin ginin.

Isa ga hawa na 20 domin kubutar da mutane a wanna yanayin "abu ne mai matukar wahala" inji shi. Idan ba an samu iska da za ta taimaka wa mutumin da aka kubutar ba, to fitowa daga ginin zai zama mai matukar hadari.

Ya zame wa jami'an kashe gobara, dole su fara aikin nasu daga kasan benen saboda yadda wutar ta yadu, kuma akwai yiyuwar cewa ginin zai iya faduwa.

Yanzu haka 'yan kwana-kwanan Landan "ba su karaya ba."

Kwamishinan kashe gobara na birnin Landan Dany Cotton ya ce. "suna duba cikin ginin lokaci zuwa lokaci domin karasa kashe wutar a cikin benayen tare da dubo mutane".

Gobarar London: Ana kyautata zaton mutane 58 sun mutu

Kwararru a fanni kiyaye gobara sun nuna cewa katakan da ke ginin ne suka taimaka wajen haddasa yaduwar wutar cikin hanzari, wanda hakan ya sa wutar ta yadu a kowane hawa na benen.

Mista Wilsher, ya ce jami'an kashe gobarar sun samu nasarar zuwa hawa na karshe na benen, "amma sai da hakan ya dauke su sa'o'i kafin su kai ga can."

A Dubai, a baya-bayannan wuta ta kama dogon gini, wanda ya hada da bene mai hawa 79 a shekarar 2015, ta yadu ne saboda katakan da ke ginin, inji wani kamfanin kashe gobara.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Bidiyon gobarar da ta kama wani bene a birnin London

Kamfanin ya kara da cewa, amma gobarar ba ta ci rayuka ba saboda yadda tsarin ginin yake, ya bai wa jami'an kashe gobara damar cin karfinta.

Kuma mazauna ginin sun samu nasarar fita ta wasu hanyoyi da ba su da wuta da kuma hayaki.

Daraktan kamfanin Sam Alcock, ya ce:"Duka-duka wutar an ci karfinta ne cikin sa'o'i bakwai, kuma mazauna benen sun samu nasarar ficewa, kuma an kashe wutar gaba daya ba tare da rasa rai ba".

Ya kara da cewa "A ganina kubutar da rayukan mutane ya ta'allaka ne ga yadda aka tsara da kuma gina bene."

Tun da farko an bai wa mazauna benen Grenfell Tower, shawarar cewa su zauna a cikin dakunansu a lokacin gobarar ta fara, kuma wani injiniya ya bayyana dalilin yin hakan.

"Za ka bai wa mutane shawara da su zauna ne idan kana da kyakkyawan kayan aiki, amma a wannan lamari na Landan, shawarar ba ta yi amfani ba".

Manyan gobara da duniya ta fuskanta a baya-bayannan.

  • Ginin Plasco, A kasar Iran, a watan Janairun 2017: Wuta ta kama benen kasuwanci mai hawa 17, a babban birnin kasar Iran, wacce ta haddasa mutuwar mutane da dama, da suka hada da jami'an kashe gobara 18, kuma ginin ya rushe. An yi zargin cewa ginin yana da matsala kafin aukuwar lamarin.
  • Gobarar Baku, a kasarAzerbaijan, a watan Mayun 2015: Mutane 16 ne suka mutu a wata gobara da ta tashi a wani gida, ciki har da yara biyar, an dora alhakin ruruwar wutar kan katakon da ke ginin.
  • Gobarar Torch, a kasar Dubai, a watan Febrairun 2015: Wuta ta kama daya daga cikin dogayen gini na duniya. Daruruwan mutane sun kubuta daga benen mai hawa 79.
  • Gobarar Krasnoyarsk, na kasar Rusha, a watan Satumbar 2014: Wutar ta lalata benen mai hawa 25. gaba daya mazauna ginin 115 sun samu nasarar ficewa daga benen, kuma ba a samu asarar rai ba.
  • Gobarar Shanghai,na kasar China, a watan Nuwambar 2010: Gobarar da ta kama benen mai hawa 28, ta hallaka mutum 53 tare da jikkata akalla mutum 90. Ma'aiakatar yada labaran kasar ta zargi masu walda ba bisa ka'ida ba da haddasa gobarar.

Jami'an kashe gobara kan yi amfani da jirage ta sama a gobarar da ta kama dogayen gine-gine, domin kashe wutar daga wajen ginin.

Amma a gobarar Landan motocin kashe gobarar ba za su iya wuce tsawon mita 32 ba, inda hakan ba zai iya bari a kashe wutar ba.

Mista Alcock, ya ce a Dubai inda suke da ginin kamar na Burj Khalifa, wanda ya kai hawa 160, suna da jiragen kashe gobara da suke iya tashi har na tsawon mita 80.

Amma gine-gine su rika samar wa 'yan kwana-kwana damar shiga cikinsa, wannan ya hada da lifta ta musamman, na da matukar muhimmanci.

Mazauna dogayen benaye a Birtaniya kamar Grenfell Tower, wadanda dakunansu ba su samu wuta ko hayaki ba a kan ba su shawara da su tsaya a wurin.

Saboda gaba daya da jami'an kashe gobarar da kuma wadanda suke kokarin fice a daga ginin suna amfani da hanya daya ne, kamar yadda wani kwararre a fannin kashe gobara ya ce.

Wani kwararre a fannin kashe gobara ya shaidawa BBC cewa: "Jami'an kashe gobara ba sa bukatar daruruwan mutane su rika saukowa, a lokacin da suke kokarin kashe wutar".

Labarai masu alaka

Karin bayani