Bam ya tashi a wata makarantar rainon yara a China

Gabshin China Hakkin mallakar hoto Reuters/CCTV
Image caption Gidan talabijin na kasar ya nuna cunkoson mutane da suka taru a kofar makarantar

Kafar yada labaran kasar China ta ce, wani abu da ya fashe a wata makarantar rainon yara ya yi sanadiyyar mutuwar mutum bakwai da kuma jikkata akalla mutum 66.

Wani jami'in kamfanin dillancin labariai na China Xinhua ya ce, bam din ya tashi a kofar makarantar a yankin Fengxian da ke gabashin lardin Jiangsu.

Ba a san yawan yaran da suka suka jikkata ba.

Ba a gano musabbabin tashin bam din ba, sai dai wani rahoton kafar yada labaran da ba a tabbatar da shi ba na cewa, yana iya kasancewa wata tukunyar gas da take wurin ajiye kayan abinci ce ta haddasa fashewar.

Al'amarin ya faru da misalin karfe 5:00 agogon kasar, a dai-dai lokacin da iyaye suke daukar 'ya'yansu daga makarantar.

Wasu hotunan da aka yada a shafikan sa da zumunta da ba a tantance ba, sun nuna manya da yara kwance a kasa.

Wani bidiyo kuma ya nuna mutanen da suka jikkkata suna rike da 'ya'yansu suna kuka, da wata mata-da kayan jikinta suka kone-cikin halin razana.

Kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya bayar da rahoton cewa, nan take mutum biyu suka mutu, wasu biyar kuma sun mutu bayan da suka jikkata. Tara daga cikin wadanda suka jikkata na cikin mawuyacin hali.

Jami'an 'yan sanda sun ce suna gudanar da bincike.

Wannan shi ne bala'i karo na biyu da ya faru a makarantar rainon yara ta China makonnin baya-bayan nan.