'Wando a hannu na kuɓuta daga masu garkuwa'

'yan sanda za su yaki masu yi garkuwa da jama'a a Najeriya Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Rundunar 'yan sandar Najeriya ta ce ta aika 'yan sanda 600 da za su yaki masu garkuwa da jama'a

Wani Matashi da aka sace tare da sauran abokan tafiyarsa a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna ya ce masu garkuwar sun doke shi a haƙarƙari da ƙafafuwansa.

Matashin wanda saboda dalilan tsaro ba za a ambaci sunansa ba ya faɗa wa BBC cewa, sai da wani a cikin ɓarayin mutanen ya cinna masa bindiga a kunne yana cewa idan ya sake cewa uffan zai harbe shi nan take.

Ya ce sun yi masa dukan ne bayan ya faɗa musu cewa ba shi da wani da zai iya fansar shi, don haka ya saddaƙar kawai.

Matashin ya ce bayan sun raba su gida biyu a cikin dare, washe gari kuma sai ya ji ana ta kiran ɗaya daga cikin masu garkuwar a waya.

"Su da bakinsu sun faɗa mana mutane a dajin nan (waɗanda masu garkuwar suka sace) sun fi ƙarfin ashirin."

Ya ce ana ta kiran shi a waya ana roƙon shi arziƙi don neman sasantawa.

"Akwai mutum ɗaya da aka kama matarsa, shi ne ya yi ƙoƙari ya ce zai kawo musu miliyan biyu. An gama komai."

Kuma ya ce ya ji shi mai garkuwar yana yi wa mutumin da yake magana da shi gargaɗin cewa kada ya sake ya je karɓar matarsa da jami'an tsaro.

"Kar ka sake ka zo da ma'aikaci, in ka sake ka zo da ɗaya wani abu ya faru. To, matarka kwananta ya ƙare."

Daga nan sai suka hau babura suka tafi, suka bar matashin da wani a hannun ɗaya daga cikinsu riƙe da bindiga, in ji shi.

Ya ce sai abokin da aka sato su tare yake ba shi shawarar ko za su gwada sa'a, su ƙwaci kansu a hannun wanda aka bar su da shi.

"Mun ji azaba ta ishe mu. Ga zafin rana, ga gajiya ga duka, ga yunwa. Tun muna kukan zuci har muka fara na ƙwalla."

Ya ce abokin tafiyarsa ya faɗa masa cewa yana ganin za su iya ƙwatar kansu a hannun ɗan garkuwar.

Matashin ya ce wata shawara ce ta zo masa, sai ya faɗa wa mai tsaron nasu cewa zai yi fitsari.

To, kuma a cewarsa ba zai bar shi ya tafi, shi kaɗai ya bar wancan a nan ba, dole sai su duka. "Yana bayana, shi kuma abokin tafiyata sai ya yi dabara ya biyo ta bayansa ya riƙe shi gam."

Daga nan sai kokawa, har Allah ya ba mu nasara a kansa.

"Mu dai ba mu kashe shi ba, Sai kowa ya nemi hanyar shi. (Ko) Allah ya fitar da wancan? (Ko) ya aka yi? Ni ban sani ba."

Ya ce shi ne ya ƙwace wayar ɗan garkuwar ya jefa a ruwa don gudun kada ya kira abokan satarsa. "Bindigar kuma a nan muka bar ta..."

Matashin ya ce ya shafe tsawon sa'a 4 da rabi yana gudu kafin ya fito kan titi daga cikin surƙuƙin daji.

"Wandona saboda ya jiƙe ya yi min nauyi. Na ga zai ɓata min lokaci sai na kwaɓe na riƙe a hannu. Na dinga yanka daji."

Labarai masu alaka