Leicester City ta sayi Harry Maguire a kan fam miliyan 17

Harry Maguire

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Maguire zai koma Leicester City ne a farkon watan Yuli

Kulob din Leicester City ya sayi Harry Maguire daga Hull City a kan fam miliyan 17, inda zai kasance a can har tsawon shekara biyar.

Dan wasan mai shekara 24, zai koma ne Leicester City ne a farkon watan Yuli.

Maguire ya ce: "Akwai dimbin kungiyoyi da suke zawarcina, amma da na gana da manajan Leicester City sai na ji na fi nutsuwa da shi."

Hakazalika, ya ce "Lecester City yana samun tagomashi kuma yana da kyakkyawar makoma."

Kulob din Leicester City ya kammala Gasar Firimiyar bana ne a mataki na 13.