An nada Ahmed Musa sarautar jagaban matasan Arewa

A ranar Alhamis ne wata kungiyar dalibai ta arewacin Najeriya ta nada dan wasan kulob din Leicester City, Ahmed Musa, sarautar jagaban matasan arewa a Kano.
Abokan arziki na ci gaba da taya dan kwallon Nigeria Ahmed Musa, murna bayan da aka nada shi sarautar Jagaban Matasan Arewa a birnin Kano da ke areacin kasar.
A ranar Alhamis ne wata kungiyar dalibai ta arewacin Najeriya ta bai wa dan wasan, wanda ke taka leda a kulob din Leicester City, wannan sarauta.
Matasa da dama ne da abokan arzikin Ahmed suka halarci bikin.
Kuma suna ta taya shi murna kan sarautar a shafukan sada zumunta.
Har ila yau, dan wasan, wanda a baya ya murza-leda a kulob din Kano Pillars, ya bude wani wurin wasanni ciki har da wasan kwallon kafar 'yar tile.