Watakila Russia ta kashe shugaban IS al-Baghdadi

A man purported to be the reclusive leader of the militant Islamic State Abu Bakr al-Baghdadi - June 2014 Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Abu Bakr al-Baghdadi na yin huduba a shekarar 2014

Ma'aikatar tsaron kasar Rasha na gudanar da bincike don gano ko daya daga cikin harin saman da ta kai a Siriya ya yi sanadiyyar mutuwar shugaban kungiyar IS.

Ma'aikatar ta ce, wata kila harin saman da aka kai na ranar 28 ga watan Mayu, ya yi sanadiyyar mutuwar Abu Bakr al-Baghdadi da kuma wasu mayakan da yawansu ya kai 330.

Ma'ikatar ta ce an shirya kai harin ne kan wata ganawa da manyan kungiyar IS suke yi a yankin da suke rike da shi a babban birnin Raqqa, da ke arewacin Siriya.

An samu rahotanni da yawa a baya-bayan nan da suke nuna cewa Baghdadi ya mutu.

Mai magana da yawun gamayyar da Amurka ke jagoranta wajen yaki da IS, Colonel John Dorrian ya ce, har yanzu Amurka ba ta tabbatar da mutuwar tasa ba.

Sannan kuma babu wani bayani a hukumance da aka samu daga gwamnatin Siriya.

A wani jawabin da ma'aikatar tsaron Rasha da kamfanin dillancin labarai na kasar ya wallafa, ya ce, kwamandojin IS 30 ne da kuma sojojinsu kimanin 300 suka halacci ganawar a Raqqa.

Sun kara da cewa, "A cewar wani bayani da yake bincike a tashoshi da dama, harin saman da aka kai ya yi sanadiyyar mutuwar shugaban IS Ibrahim Abu-Bakr al-Baghdadi, wanda shi ma ya halarci ganawar."

Dama dai ba a san takamaiman inda Baghdadi ya ke ba na wani lokaci, koda yake an yi amanna cewar yana Mosul a Iraki, tun kafin gamayyar da Amurka ke jagoranta ta fara kokarinta wajen kara kwace birnin a watan Oktobar shekarar 2016.

Kamfanin dillanci labarai na Reuters ya bayar da rahoton cewa, a baya-bayan nan an fi yakinin cewa, "yana boye a wata hamada mai nisan tafiyar dubban kilo mita," maimakon zama a Mosul ko Raqqa.

Tun lokacin da ya fito da wani sabon bidiyo a shekarar 2014, yana da'awar kafa daular IS ba a sake ganin bayyanarsa ba, inda yake bayar da huduba a Mosul bayan da IS suka kwace ikon birnin.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Dubun-dubatar mutane sun bar Raqqa a yayin da fada ke kamari

Tun daga wannan lokacin, kungiyar ta yi asarar manyan birane masu yawa, kuma suke fuskantar matsin lambar harin sama daga rundunar da Rasha ke jagoranta da kuma Amurka da masu mara mata baya.

A watan Maris, sakataren wajen Amurka, Rex Tillerson ya ce, "an kashe kusan dukkan mataimakan Baghdadi."

Ya kara da cewa, "Dama komai lokaci ne, kafin Baghdadi ya gamu da ajalinsa".

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ma'aikatar harkokin wajen Iraki ta fitar da hoton Baghdadi a watan Janairu a shekarar 2014

Wane ne Al-Baghdadi?

Ana tunanin cewa yana amfani da Baghdadi ne amma ba shi ne ainihin sunansa ba, an yi amanna cewa an haifeshi a Samarra da ke arewacin Baghdad, a shekarar 1971.

Rahotanni na bayyana cewa, malami ne a wani masallacin birnin garin, tun lokacin da Amurka ta jagoranci kai hari a shekarar 2003.

Wasu suna da yakinin cewa, dama can yana cikin masu jihadi tun lokacin mulkin Saddam Hussein. Wasu kuma na cewa dama yana da tsattsauran ra'ayi a lokacin da yake sansannin Bucca na tsawon shekara hudu, wani gidan yarin Amurka da ke kudancin Iraki, wanda mafi yawancin kwamandojin al-Qaeda suke tsare.

Ya zama shugaban al-Qaeda a Iraki, daya daga cikin kungiyoyin da daga baya suka zama kungiyar IS a Iraki a shekarar 2010.

A watan Oktobar shekarar 2011 ne, Amurka ta tabbatar da Baghdadi a matsayin "Dan ta'adda". Ta kuma yi alkawarin bayar da dala miliyan 25 ga duk wanda ya kawo bayanin kama shi ko mutuwarsa.

A watan Yunin shekarar 2014 ne IS ta kwace Mosul, babban birnin na biyu a Iraki, kafin yin da'awar kwace babban birnin, da kuma kaddamar da munanan hare-hare a biranen da ke yammacin kasar, da suka hada da birnin Paris a watan Nuwambar 2015.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Wani mazaunin Raqqa ya bayyana yadda rayuwa take a karkashin IS

Labarai masu alaka

Karin bayani