Kun san shafin Facebook ɗin da matan Nigeria ke baje-kolinsu?

Lola Omolola and Mark Zuckerberg Hakkin mallakar hoto FIN
Image caption Omolola da Zuckerberg

Wannan shafi na ɗaya daga cikin shafuka masu bunƙasa da samun ɗimbin mabiya, wanda a dalilin haka har Shugaban Facebook Mark Zuckerberg ya taɓa ganawa da wacce ta ƙirƙiro shafin mai suna, FIemale In Nigeria, wato FIN a taƙaice.

Shin mene ne FIN?

FIN, wani shafin Facebook ne na "na sirri", wanda a baya-bayan nan ya samu fiye da mambobi miliyan daya, kuma yawancinsu 'yan Najeriya ne.

Amma wani sirri ne wadda ta kirkireshi, Lola Omolola, take so ku san komai game da shi, in dai har ke mace ce.

Mis Omolola, ta yi bayanin cewa, "Amintaccen shafi ne, ga matan da suke da wani abin cewa."

"Ba lallai ne ku yarda ba, amma labarinta ne, tana iya bayyana shi," in ji ta.

Shafi ne da yake warware bayanai karara, inda mata suke bayyana labaransu da abin da yake damunsu, ko kuma wani abu da suke jin tsoron fada wa wani.

Ba mu bayar da damar sakaya suna ba, mambobin na amfani da sunansu na ainihi wajen yada wani bayani.

Kuma labaran na da matukar ban mamaki, kodayake sun kasance suna da tsananin sirri.

Ban dade da zama mamba a shafin ba, amma ni shaida ce, na karanta labarai na cin zarafin mata, da labaran tashin hankali, da cin zarafin kananan yara, da fyade.

Wata mata ta yi magana game da lokacin da ta gaya wa iyayenta cewa, tana da ciki kuma a lokacin ba ta yi aure ba tana 'yar shekara 17, wata kuma ta bayar da labarin yadda mahaifiyarta ta haƙura ta karbi kaddararta ta zama 'yar madigo bayan shekaru masu yawa.

Kamar matar da ta sha kunya a rana ta farko a gaban wani taro, ko wata budurwa da ta sace mukullan wani direban mota, bayan da ya yi karo da motarta kuma yaki ya ba ta hakuri.

Yawancin labaran na yin magana ne a kan wani darasi da 'yan Najeriyar.

Hakkin mallakar hoto Lola Omolola
Image caption Wasu mambobin shafin Fin sun gana da junansu

Mis Omolola ta ce, "Matan Najeriya sun zama ginshiki a wannan bangare, saboda ni ma macen Najeriya ce."

Mis Omolola wata tsohuwar 'yar jarida da ta bar Najeriya ta koma Amurka a farkon shekarar 2000, a lokacin tana da shekara 24, kuma ta bude wannan shafi a 2015.

Ta fara tunanin kamatar fara yin wani abu na dan wani lokaci, kafa wata kungiya da matan Najeriya za su samu damar yin magana a kan batutuwan da suka shafesu. Kuma sace 'yan matan Chibok ne ya ja hankalinta.

Ta ce, "Na san abin da ya haddasa hakan".

"Idan ka girma a wurin da ba a sauraron ra'ayin mace, saboda mutane na daukar cewa hakan ba zai haifar da abin kirki ba.

Ba ta yi mamaki ba na cewa wasu gungun maza za su iya garkuwa da kuma bautar da 'yan matan, saboda ba sa kallonsu a matsayin daya suke da su.

"Na fahimci cewa tsakanin shekara uku zuwa shida, duk lokacin da yarinya ta fara nuna wani alamu na sanin ciwon kai, za ta yi shiru. Duk lokacin da na fadi wani abu zan ganshi a zahiri

"Wadanda suke cikin wannan hali suna zuwa ne daga wurin yayyensu, ko kawunansu, wasu ma iyayensu mata, amma ba wanda za a samu daga wuirn mahaifinsu."

Babanta dan kasuwa ne, amma ba kullum yake fita ba, kuma yana yawan zama a gida tare da yara, idan mahaifiyarta ta tafi aiki.

Ta ce, "Ba mu taba fuskantar bambancin jinsi ba".

"Yanzu na gano irin kokarin da dole ya kamata mu yi."

Hakkin mallakar hoto Lola Omolola
Image caption Mambobin shafin na sakewa sosai da junansu

An bude shafin Fin ne don mata su dinga tatttauna batutuwan da suka shafesu, babban matsalar da take damunmu ita ce yadda ake cin zarafin mata, kuma Mis Omolola na kallon matsalar da a baki kawai ake fadarta.

Sai dai mata sun fi mayar da hankali a kan bayar da labaransu na kansu.

Yanzu haka shafin ya zama wurin da mutane suke sanin abubuwan da ba su san da su ba a baya.

Ta ce, "Lokacin da muka bude shafin na yi kuka, na kasa cin abinci. Saboda na ji labaran da ban taba tunanin jinsu ba".

"Akwai matan da suka shafe shekara 40 ana muzguna musu, amma ba su taba gaya wa kowa ba. Ba wanda zai iya zama cikin irin wannan hali".

Yanzu haka shafin na samun daruruwan masu son yada labari kowacce rana, sai dai shafin na karkashin kulawar mutum 28 ne kawai.

Fin na da tsauraran dokoki. Ba a yarda mambobin su yanke wa junansu hukunci a tsakaninsu ba ko a kan mene ne. Duk wani sharhi ko batu da aka yada wanda bai dace ba, za a cire shi a cire mutumin da yasa.

Mis Omolola ta ce, "Na fahimci irin wadannan mutane da suke kokarin kawo nakasu a rayuwar mata, sun shiga shafin."

"Suna cikin tsananin son biyan bukatar ransu," in ji ta.

A al'ummmar da suke da tsaurin addini kamar Najeriya, ba zai yiwu a bayyana 'yancin jima'in mata ba tare da samun suka ba.

Wasu mambobin sun yi kokari wajen yin sharhi da kawo hujjoji daga bible wanda suke haramta daukar matakan mata.

Ta ce, "Mun haramta bayar da shawara ko ko wani bayani da ya shafi addini, hakan ya saba wa dokokinmu, Fin ba wurin yin ibada ba ne."

Hakkin mallakar hoto Lola Omolola
Image caption Lola Omolola ta ce ba kudi take nema da shafin ba

Mutane sun alakanta shafin da alamar shedanci wanda yake ba ta mata matasa.

Mis Omolola ta ce, kungiyoyin coci sun sun sha yunkurin wargaza shafin. Amma ba ta damuwa.

Ta ce, "Yawancin mutane suna zaton ce-ce-kucen da aka yi zai kasheni, sun kasa gane cewa hakan ma yana kara min kwarin gwiwa."

Bayan tara dimbin miliyoyin mambobi tare da ganawa da Mista Mr Zuckerberg, me kungiyar Fin take shirin yi?

Mis Omolola na da burin fadada shafin zuwa wani ajin na daban, ta samar da cibiyoyin da mata za su rika zuwa suna bayyana wani abu da suke da masaniya, a kansa cikin kwanciyar hankali.

Sai dai hakan wata kila zai dau lokaci mai tsawo.

"Yana bukatar kudi, kuma ni ba ni da kudi a yanzu, ko kudin hayar gidana ba na iya biya," in ji ta.

Wannan ne abun da suka tattauna da Zuckerberg, kuma tana tsammanin har yanzu shafin Facebook bai bayar da wani kudi ba, har yanzu tana tattaunawa a kan yadda za ta kara fadada shafin.

Ta ce, tun daga rana ta farko ta fara samun gayyata daga kamfanoni wadanda suke son tallata shafin, amma ta ki yarda ta bayyana labaran matan.

Kuma wannan ne karo na farko da ta yi wata tattaunawa a kansa.

Karin bayani