Ambaliyar ruwa ta kashe yara a Niger

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Gidaje sun rushe, tituna kuma sun lalace

A kalla yara tara ne suka mutu sakamakon rushewar da gidaje suka yi a Yamai babban birnin jamhuriyyar Nijar, a dalilin mamakon ruwan sama da aka yi.

Ruwan ya jawo ambaliya mai tsanani tare da lalata abubuwa da dama da suka hada da daya daga cikin manyan kasuwannin birnin.

Kamfanin dillancin labarai na AP ya ruwaito wani babban jami'in gwamnati a birnin yana cewa, gidaje sun rushe a sassan birnin daban-daban inda hakan ya yi sanadin mutuwar mutanen da ke cikin gidajen.

A watan da ya gabata ne Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa mutane 106,000 ne ke fuskantar barazanar masifar ambaliya a Nijar.

Wata mata ta shaida wa wata kafar talbijin ta kasar cewa uku daga cikin 'ya'yanta hudu sun mutu sakamakon faduwar da katangar makwabtansu da suka fake ta yi a kansu.

A ranar Talata ma wasu gidajen talbijin biyu Tele-Sahel da Tal-TV sun tsayar da watsa shirye-shiryensu sakamakon yadda ruwa ya yi ambaliya cikin dakunan watsa shirye-shiryen nasu.

Wasu rahotanni daga wasu jaridun Najeriya ma na cewa abin ya shafi harkokin sufuri tsakanin iyakar arewacin Najeriyar da Nijar na tsawon kwanaki kadan, saboda yankewar da gadoji biyu suka yi a yankin Mokwa.

Wani mai amfani da intanet ya wallafa hotuna da ke nuna yadda wata tankar dakon mai da sauran ababen hawa suka tsaya cak saboda karyewar da gada ta yi.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN, ya ce, gwamnatin Nijar ta sanya dokar ta baci kan titunan gwamnatin tarayyar kasar saboda karyewar gadojin.

NAN ya ruwaito kwamishinan yada labarai na Yamai Jonathan Vatsa na cewa: "Akwai bukatar masu amfani da tituna su yi taka tsan-tsan su kuma dauki matakan kariya a yayin da suke tafiya don gudun afkuwar wani abu. Manyan titunan gwamnatin tarayyar jamhuriyyar a yanzu ba su da tabbas.

"Ina shawartar direbobin manyan motoci da sauran ababen hawa su dinga kula sosai a lokacin da suke tunkarar gada."

Ba a dade da fara samun ruwan sama a Nijar ba, wanda a kan shafe a kalla wata uku ana yin sa.

A bara ambaliyar ruwa ta shafi dubban mutane ta kuma yi sanadin mutuwar gomman mutane, mafi yawanci a yankunan hamada na Agadez da Tahoua.

Labarai masu alaka

Karin bayani

Labaran BBC