Ronaldo 'na son barin' Real Madrid

Real Madrid forward Cristiano Ronaldo Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Cristiano Ronaldo ya shafe shekara takwas a Madrid

Wata majiya ta kusa da Christiano Ronaldo ta shaida wa BBC cewa dan wasan ya fusata kuma yana son barin Real Madrid bayan an zarge shi da zambar haraji.

Masu gabatar da kara na kasar Spaniya sun zargi Ronaldo mai shekara 32 da kin biyan hukumomi harajin da ya kai miliyoyin euro, zargin da Ronaldon ya musanta.

Majiyar ta kara da cewa "Yana jin shi yana da gaskiya, yana da É—abi'a mai kyau kuma ya yi komai yadda ya kamata, saboda haka bai gane (tuhumar) ba."

"Ran shi ya baci matuka, kuma ya fusata sosai."

Majiyar ta kara da cewa: "Ba ya son zama a Spaniya. yanzu haka yana son tafiya ne."

Ronaldo, wanda ya koma Madrid daga Manchester United kan kudi fam miliyan 80 a shekarar 2009, ya sa hannu kan kwantiragin shekarar biyar da kungiyar da ta lashe gasar zakarun Turai a watan Nuwamban 2016.

China ka iya kasancewa inda zai nufa, amman masu ba wa dan asalin Portugal din shawara sun fi son ya zauna a Turai, ko ya je Paris St-Germain ko kuma ya dawo gasar Firimiya.

Ronaldo, wanda ya taimaka wa Madrid wajen lashe gasar zakarun Turai sau uku, ana zargin shi da laifin kin biyan harajin da ya kai fam miliyan 13 tsakanin 2011 da 2014.

Madrid ta fitar da sanarwar da ke cewa ta yarda da shi kuma sun yi imanin cewa zai tabbatar da gaskiyarsa.

Karin bayani

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba