Nigeria: INEC ta yi wa sababbin jam'iyyu rijista

INEC Hakkin mallakar hoto Twitter
Image caption Jam'iyyu 95 ne suka nemi INEC ta yi musu rijista

Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya (INEC) ta yi wa sababbin jam'iyyu guda biyar rijista.

Sababbin jam'iyyun da suka samu rajistar su ne, Young Progressive Party (YPP), da Advanced Peoples Democratic Alliance (APDA), da New Generation Party of Nigeria (NGP), da All Democratic Peoples Movement (ADPM) da kuma Action Democratic Party (ADP).

An wallafa Shugaban hukumar Farfesa Mahmood Yakubu yana gabatar da takardun shaidar rajistar ga sababbin jam'iyyun biyar, a shafin twitter hukumar.

Hukumar ta ce kungiyoyi 95 ne suka gabatar da takardun neman rajistar, amma jam'iyyu biyar ne suka cika ka'idar dokar tsarin yin rajistar.

A shekarar 2019 ne Najeriya za ta gudanar da babban zaben kasa.

Labarai masu alaka