Mawaƙiyar da mutum miliyan 100 ke bin shafinta

Katy Perry da Justin Bieber
Image caption Mawaƙan biyu su ne suka fi kowa yawan mabiya a shafin sada zumunta na Twitter

Wata mawaƙiya 'yar Amurka, Katy Perry ta zama mutum na farko a duniya da ya samu yawan mabiya har miliyan 100 a shafin sada zumunta na Twitter.

Shafin ya wallafa wani hoton bidiyo na jerin saƙwannin da ta buga tun bayan buɗewarta a shekara ta 2009 tare da wani saƙo da ke cewa 'Yau mun shaida #WITNESS abin tarihi."

Kalmar 'Witness' ɗin kuma ta kasance sunan sabon faifan waƙoƙi na mawaƙiya Perry.

Mawaƙi ɗan ƙasar Kanada Justin Bieber ne ke rufa mata baya a yawan mutanen da ke binsa a shafin Twitter da adadin sama da miliyan 96.

Sai tsohon shugaban Amurka, Barack Obama a matsayi na uku da masu bin shafinsa kusan mutum miliyan 91.

Labarai masu alaka