An kashe 'yar sandan Isra'ila bayan wani hari

An Israeli policewoman on duty in Jerusalem, 16 June Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption 'Yan sanda dauke da manyan makamai suna ci gaba da sintiri a wurin da abin ya faru

Yan sandan Isra'ila sun kashe wasu Falasdinawa uku bayan wani hari da aka kai da wuƙa a birnin Kudus, wanda ya yi sandiyar mutuwar wata 'yar sandan Isra'ila.

'Yan sanda sun ce biyu da cikin Falasdinawan sun kai wa 'yar sandan hari ne da bindigogi da kuma wukake, yayin da na ukun ya daba mata wuka.

Har ila yau, 'yan sandan sun ce mutane biyu daga cikin maharan 'yan kimanin shekara 18 ne, yayin da na ukun ya kai shekara 31, dukansu sun fito ne daga Gabar Yamma da Kogin Jordan.

Akwai dubban Musulmi masu ibada a birnin Kudus saboda sallar Juma'a da suke yi a Masallacin Kudus wadda shi ne na uku mafi daraja ga Musulmi.

Sai dai yayin watan azumin Ramadan Isra'ila ta sasauta takaicin zirga-zirga ga Falasdinawan Gabar Yammacin Kogin Jordan, inda take barinsu kai ziyara birnin Kudus.