Abin da ya sa mata ke sa farin kaya ranar Laraba a Iran

masu gwagwarmaya Hakkin mallakar hoto MY STEALTHY FREEDOM
Image caption Masu fafutikar na sanya farin mayafi da nufin nuna adawa da tsarin sanya tufafi

A kasar Iran wani sabon maudu'i a shafukan sada zumunta wanda ke adawa da sabuwar dokar da ta tilasata wa mata sanya kallabi yana ci gaba da samun tagomashi.

Ta hanyar amfani da maudu'in #WhiteWednesdays wato (Fararen ranakun Laraba), 'yan kasar na ci gaba da wallafa hotuna da bidiyon kansu sanye da farin dan kwali ko karamin farin mayafi a wata alama na nuna adawa.

Masih Alinejad ce ta fara sabuwar dabi'ar, wacce ta kirkiri shafin My Stealthy Freedom, da ke adawa da tilasta bin tsarin sanya tufafi da hukuma ta bukata.

Kafin juyin-juya halin addinin kasar a shekarar 1979, yawancin matan Iran na sanya tufafi irin na Turawa, da suka hada da kananan siket da kananan riguna, amma kuma wannan duk ya sauya lokacin da marigayi Ayatollah Khomeini ya karbi ikon kasar.

Ba wai tilasta wa mata rufe gashin kai kadai aka yi ba, wanda ya yi daidai da koyarwar addinin Musulunci, har ma tilasa ta musu daina yin kwalliya, da kuma fara sanya dogayen mayafai da za su rufe har kafafauwansu.

Fiye damata da maza 100,000 suka fita a kan titunan kasar domin nuna adawarsu da wannan sabuwar doka a shekarar 1979, adawar da har yanzu ba a daina ta ba.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Masu tsattsauran ra'ayin addini a Iran na son kasar ta tilasta dokar sanya tufafi

A tsawon shekara uku da ta yi da fara aiki, shafin My Stealthy Freedom ya samu sama da hotuna da bidiyo 3,000 wanda ke nuna matan ba tare da dan kwali ko mayafi ba.

A yayin da shafina na My Stealthy Freedom ke wallafa hotunan da ake dauka a asirce saboda gudun fushin hukumomin, maudu'in #whitewednesdays ya bai wa mata dama su bayyanar a adawarsu a fili.

A yanzu da yake makonsa na biyar da kafuwa maudu'in na #whitewednesdays ya samu karbuwa, inda aka aike da bidiyoyi sama da 200 zuwa ga shafin misis Alinejad a makonnin biyun farko, wasu daga cikin su na da yawan wadanda suka kalla akalla 500,000.

Wata wacce ta wallafa bidiyonta a shafin yayin da take tafiya a kan titi ta ce "Ina matukar jin dadin adawa da wannan mataki, ina so in fada muku irin wahalar da aka sani, sun tilasta min sanya hijabi tun ina 'yar shekara bakwai bayan kuma ban taba jin ina son amfani da shi ba" tana magana ne lokacin da take kwance dan kwalin kanta.

Hakkin mallakar hoto MY STEALTHY FREEDOM
Image caption Wasu mata na fargabar bayyana ra'ayinsu a maudu'in na #whitewednesdays

Misis Alinejad ta ce ta ji dadi da wannan zanga-zanga mai cike da karsashi- wasu matan sun tura bidiyon kansu suna tafiya a kan tituna ba tare da sanya kallabi ba.

"Lokacin da na nuna damuwata game da kariyar wata mai fafutika, sai ta ce ta gwammace ta rasa aikinta da ta ci gaba da zama karkashin abin da ta kira zaluncin da matan Iran ke fuskanta na tsawon shekaru 38," in ji Alinejad

Hakkin mallakar hoto MY STEALTHY FREEDOM
Image caption Gwagwarmayar ta shiga kasashe da dama

A ganin Misis Alinejad, wannan wani gagarumin aiki ne mai farin jini. Ta kaddamar da aikin da kanta, tare da taimakon wasu masu sadaukar da kai a lokuta na musamman, kuma wani lokaci sukan bata dare wajen ganin sun shugar da bidiyoyin cikin shafin.

Mafiya yawan hotunan da bidiyoyin suna zuwa ne daga cikin kasar Iran, amma Misi Alinejad na samun taimako daga mazauna Saudiyya (kasar da daura mayafin yake wajibi) da kuma wasu wuraren da suka hada da nahiyar Turai da Amurka.

Hakkin mallakar hoto MY STEALTHY FREEDOM
Image caption Wasu mata ciki har da wadanda ba Musulmi ba na nuna goyon bayansu ga 'fafutikar'

Wata mata a Afghanistan ta bayyana ra'ayinta game da wannan fafutikar da kuma goyon bayanta, duk da cewa ita kanta tana tsoron wallafa hotunanta ba tare da sanya hijabi ba.

Sanya mayafi ba wajibi ba ne a dokar kasar Afghanistan, amma iyalai na tilasta wa mafiya yawan 'yan mata da manyan mata sanya shi.

Labarai masu alaka