An yanke wa mutum 30 hukuncin kisa a Masar

Mista Barakat Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Marigayi Barakat ya gurfanar da dubban masu tsatstsauran kishin Islama a gaban kuliya

Wata kotu a birnin Alkhahira na kasar Masar ta yanke wa mutum 30 hukunci kisa bayan ta same su da hannu a kisan babban mai gabatar da kara na kasar, Hisham Barakat.

An kashe Mista Barakat ne bayan wani harin bam da aka kai wa motarsa a watan Yunin shekarar 2015.

Marigayin shi ne babban jami'an gwamnatin kasar da aka taba kashewa a 'yan shekarun nan.

Mista Barakat ya gurfanar da dubban masu tsatstsauran kishin Islama a gaban kuliya, tun bayan hanbarar da gwamnatin kasar Masar da ke samun goyon bayan Kkungiyar 'Yan uwa Musulmi a shekarar 2013.

Daruruwan masu tsatstsauran kishin Islama ne aka yanke wa hukuncin kisa, ko daurin rai da rai a wani yunkuri da murkushe masu goyon bayan Kungiyar 'Yan uwa Musulmin, wadda gwamnatin kasar ta haramta.

Masar ta dora alhakin kisan Mista Barakat a kan Kungiyar 'Yan uwa Musulmi da kuma Kungiyar Hamas da ke zirin Gaza.

Amma duka kungiyoyin biyu sun musanta hannu a kisan marigayin.

Sai dai ba za a zartar da hukuncin kotun ba, har sai bayan amincewar majalisar kolin malaman kasar.

Har ila yau bayan amincewar majalisar malaman, wadanda aka yi wa shari'ar za su iya daukaka kara.

Labarai masu alaka