Gobarar London: Ana kyautata zaton mutane 58 sun mutu

london fire Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mutane talatin ne aka tabbatar sun mutu a gobarar kawo yanzu

'Yan sanda a nan London sun ce mutane hamsin da takwas ne yanzu ba a gani ba, kuma ana kyautata zaton bu da rai, bayan mummunar gobarar da ta ta shi a dogon ginin Grenfell ranar Laraba.

Wani mai magana da yawun 'yan sandan ya ce binciken da suke yi na gano wadanda gobarar ta shafa a ginin, zai iya daukan su makonni ba su gama ba.

Mutane talatin ne kawo yanzu aka tabbatar sun mutu a gobarar.

Bayan ta gana da wasu da gobarar ta shafa a gidanta, Firayiministar Burtaniya, Theresa May ta amsa cewa, lallai ba a ba mutanen isasshen taimako da bayanai ba, bayan da aka kashe gobarar.

Ta ce ta bayar da wa'adin makonni uku, na a tabbatar an nemawa dukkan wadanda gobarar ta shafa gidajen zama a kusa.