Alkali ya yi watsi da shari'ar Bill Cosby

Bill Cosby Hakkin mallakar hoto Evan vucci
Image caption Bill Cosby ya musanta cin zarafin wata mata ta hanyar lalata shekaru 13 da suka wuce

Wani alkali a Amurka ya yi watsi da shari'ar da ake yi wa Bill Cosby, fitaccen jarumin fina-finan nishadantarwan nan da aka tuhuma cin zarafin wata ta hanyar lalata.

Alkalan kotun su bakwai, sun kasa yanke hukunci bayan sun shafe fiye da sa'o'i hamsin suna muhawara.

Fuskar Mista Cosby ba ta canja ba, lokacin da babban alkalin kotun ya bukaci sauran alkalan da su kama gabansu kawai, sannan ya ce Mista Cosby zai ci gaba da zama da belin shi.

Mai shigar da karar ya shaida wa taron 'yan jarida cewa zai bukaci a sake bude shari'ar ba tare da bata lokaci ba.

Mista Bill Cosby dai, ya musanta cewa ya bugar da wata mata da abun sa maye, sannan yayi lalata da ita a gidan shi dake Philadelphia shekaru 13 da suka wuce.