Wani sojan Afghanistan ya hari kan dakarun kasashen waje

Sojoji a sansaninsu da ke Afghanistan Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Sojoji a sansaninsu da ke Afghanistan

Wani sojan Afghanistan ya kai hari kan dakarun kasashen waje a sansaninsu, inda ya raunata wasu sojin Amurka.

Wani jami'i ya tabbatarwa BBC cewa lamarin ya faru ne ranar Asabar a sansanin da ke arewacin kasar.

Sai dai wani kakakin kwamandodjin yakin Amurka da ke birnin Kabul ya yi watsi da rahotannin da ke cewa an kashe sojin Amurka.

Amma dai wasu sojojin Amurkar da ba a fadi yawansu ba sun ji rauni lokacin da sojan na Afghanistan ya bude wuta a sansanin Shaheen.

Rundunar sojojin kungiyar tsaro ta Nato ta ce maharin ya kashe sojan Afghanistan daya sannan ya jikkata wani a lokacin harin da ya faru da karfe 09:30 GMT.

An kai harin ne mako guda bayan wani kwamandan sojin Afghanistan ya harbe har lahira sojojin Amurka uku a gabashin kasar.

Kungiyar Taliban ta ce ita ke da alhakin kai harin.

Labarai masu alaka

Karin bayani