Ɗaurin shekara nawa za a yi wa Ronaldo, Messi da Neymar?

L-R Cristiano Ronaldo, Neymar and Lionel Messi (file pics) Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption 'Yan wasan uku (Hagu-zuwa Dama) Ronaldo, Neymar and Messi

Kasar Spain ta dauki 'yan wasa uku mafiya bajinta a fagen kwallon kafar duniya, su ne Cristiano Ronaldo na Real Madrid da Lionel Messi da Neymar na Barcelona kuma dukkan su suna nuna kwarewarsu a gasar La Liga.

A shekara daya da ta wuce, masu sha'awar kwallon kafa sun saba da jin yadda 'yan wasan uku suka tsinci kansu a batun zargin guje wa biyan haraji da wasu zarge-zarge na aikata laifukan da ke da alaka da kudi a kotunan Spain.

Ba su kadai ne 'yan wasan da aka gurfanar a gaban kotunan Spain ba. A 2016, an yanke hukuncin daurin jeka-gyara-halinka na shekara daya kan dan kasar Argentina Lionel Messi da takwaransa a kulob din Barcelona Javier Mascherano saboda laifin cuwa-cuwa wurin biyan haraji.

'Yan wasa uku, shari'a uku

A bara ne aka samu Lionel Messi da mahaifinsa Jorge da laifin kin biyan harajin da ya kai €4.1m (£3.6m; $4.6m) a tallan amfani da hotonsa, wanda wasu kamfanoni da ke taimakawa mutum kauce wa biyan haraji da ke Belize da Uruguay suka jagoranta.

An yanke wa kowannensu daurin wata 21 a wani hukunci da kotun kolin Spain ta tabbatar da shi a kwanan baya.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An tuhumi Messi da mahaifinsa Jorge da kaucewa biyan haraji a 2016

Wata kotun da ke Barcelona ce za ta yanke hukunci kan ko za a soke hukuncin da aka yanke musu bisa la'akari da al'adar Spain ta janye hukunci kan mutumin da ya aikata laifi a karon farko idan daurin da aka yanke masa bai wuce shekara biyu ba.

Masu shigar da kara sun bukaci kotu ta yanke wa Neymar, wanda aka wanke daga tuhuma, hukuncin daurin shekara biyu sannan a ci tararsa €10m kana ake yi masa shari'a saboda zargin da ake yi masa na cin hanci lokacin komawarsa Barcelona daga kulob din Santos na Brazil a 2013.

Yanzu kuma Ronaldo ya kasance dan wasa na uku kuma na karshe a cikin 'yan ukun da ke gasar La Liga da yake fuskantar zargin aikata manyan laifuka, bayan masu shigar da kara sun bayar da sanarwa cewa suna bibiyar tsohon dan wasan na Manchester United mai shekara 32 kan laifuka hudu da suka shafi kin biyan haraji.

Wata majiyar da ke kusa da Ronaldo ta shaida wa BBC "ransa ya yi matukar baci" kan wadannan zarge-zarge. "Ba ya so ya zauna a Spain. A yanzu so yake ya bar kasar," in ji majiyar.

Me ya sa aka sauya dokoki?

Lokacin da David Beckham ya koma Real Madrid a 2003, an soke masa biyan haraji a wani mataki na jan hankalin 'yan wasan kasashen waje zuwa Spain.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An yafe wa manyan 'yan wasan Real Madrid kamar su Beckham da Zidane biyan haraji

A wancan lokacin tattalin arzikin Spain na tsaka da bunkasa, lamarin da ya sa 'yan wasa irinsu Zinedine Zidane da Luis Figo suka ci bagas, kafin zuwan Cristiano Ronaldo da Lionel Messi.

A 2010 aka soke wannan garabasa kan duk dan wasan da albashinsa ya zarta €600,000, kuma tun daga lokacin ne masu sanya ido kan biyan haraji suka matsa lamba kan masu yin amfani da kamfanonin kasashen waje wurin zille wa biyan haraji.

"Bambancin da ke tsakanin kin biyan haraji da kauce wa biyan haraji yana da kyau a wadannan yanaye-yanaye. A shekarun baya hukumomin karbar haraji na Spain sun matsa kaimi kan 'yan wasan kwallon kafa da kamfanoninsu, suna duba yiwuwar ko akwai batun zagon kasa," in ji Carlos Cruzado shugaban gamayyar kungiyoyin karbar haraji, Gestha.

Lamarin Neymar daban yake da na sauran. Ana zarginsa da yin kumbiya-kumbiya a kan kudin kwantaraginsa, amma kasarsa Brazil ta same shi da laifin cuwa-cuwar haraji a lokacin da yake yi wa kulob din Santos wasa.

Tuhumar da ake yi wa Messi da Ronaldo iri daya ce. Ana zarginsu dukkansu da zille wa biyan haraji a kwangilar amfani da hotunansu wurin yin tallace-tallace ta hanyar yin amfani da kamfanonin kasashen waje wurin boye kudinsu.

Masu shigar da kara sun zargi dan kwallon na Real Madrid da zille wa biyan harajin €14.7m tsakanin 2011 da 2014ta hanyar wani kamfanin kasashen waje Tollin Associates, wanda aka yi wa rijista a British Virgin Islands.

Messi dai ya ce mahaifinsa ne yake tafiyar da harkokin kudinsa don haka ba shi da masaniyar cewa ba a biyan haraji a dukiyarsa.

Sun kare kansu

Alkali ya shaida wa Lionel Messi cewa rashin sanin harkokin kudinsa ba hujja ce da za ta fitar da shi daga zargin da ake yi masa ba.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Neymar ya kwashe minti 90 a gaban wani alkalin kotun Madrid a watan Fabrairun 2016

Neymar ya musanta aikata ba daidai ba sannan ya gaya wa kotun da ke bincike a kansa cewa mahaifinsa da masu hulda da shi ne ke tafiyar da harkokin kudinsa.

Wakilan Cristiano Ronaldo da kuma lauyoyinsa sun ce ja-in-jar kawai ta faru ne a kan lissafin yawan kudin da ya kamata ya biya haraji ne amma babu wata niyya ta yin coge.

Sun kara da cewa "Babu wata niyya ta zille wa biyan haraji.. Babu wata niyya ta boye wani abu".

Sun jaddada cewa ya biya gwamnatin Spain kashi 20 cikin 100 na kudin da ya samu daga tallan da ake yi da hotunansa, duk da yake ya samu fiye da kashi 90 na kudin ne ba a kasar ba.

Za a daure su?

Da alama ba za a daure Neymar da Lionel Messi a gidan yari ba saboda al'adar Spain ta janye hukunci kan mutumin da ya aikata laifi a karon farko idan daurin da aka yanke masa bai wuce shekara biyu ba, ko da kuwa an samu Neymar da laifi.

Amma batun Cristiano Ronaldo yana da bambanci. Masu shigar da kara sun ce uku cikin laifuka hudu da ake zarginsa da aikatawa manya ne, kuma kowannensu na iya jawo masa daurin shekara biyu a gidan yari.

Sai dai alkali na bukatar tantance zarge-zargen da masu shigar da kara suka yi masa, kuma hakan ka iya daukar watanni ko ma shekaru da dama.