Tarihin tashe a ƙasar Hausa

Tashe Hakkin mallakar hoto Getty Images

Tashe yana daya daga cikin al'adun Hausawa na asali kuma ana yinsa ne a cikin watan azumin Ramadan.

Shugaban Sashen Harsuna na Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano, Malam Yusuf Muhammad, ya ce kalmar tashe ta samo asali ne daga kalmar tashi wato tashi domin sahur yayin daukar azumi.

"Wasannin tashe sun samo asali ne daga Nalako, wanda sarki ne yake nada shi wato a matsayin sarkin gwagware - wadanda suka dade ba su yi aure ba," in ji shi.

Nalako yana kewayawa ne yana wasanni don tashin gwagware daga bacci saboda ba su da matan da za su rika tashinsu.

Har ila yau, ya ce tashe yana taka muhimmiyar rawa wajen adana tarihin Hausawa, kodayake, ya ce zamani ya fara yin tasiri ga al'adar.

Ga cikakken bayanin da ya yi wa BBC a shirin Amsoshin Takardunku

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Malam Yusuf Muhammad yana bayani kan tashe

Labarai masu alaka