Jay-Z ya samu 'yan tagwaye

Beyonce da Jay-Z

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Beyonce da mijinta Jay Z sun yi aure ne a shekarar 2008

Shahararriyar Mawaƙiyar Amurka Beyonce ta haifi tagwaye, kamar yadda wata kafar yada labarai a Amurka ta bayyana.

Sai dai ba a bayyana ranar da ta haifi jirajiran ba.

Hakazalika ba a san abin da haifa ba wato ko maza ne, ko kuma mata.

A watan Fabrairun da ya wuce ne mai jego Beyonce ta bayyana cewa tana dauke da juna biyu a shafinta na Instagram.

Ba wannan ce haihuwar mawakiyar ta farko ba tare da mijinta Jay-Z, suna da 'ya mai shekara biyar mai suna, Blue Ivy.

Sai dai Beyonce da Jay-Z ba su fito fili sun tabbatarwa duniya labarin haihuwar ba.