Abubuwan da suka faru a Afirka a makon jiya

Ga wasu hotuna da aka zabo na abuuwan da suka faru a nahiyar Afirka a makon jiya.

Hakkin mallakar hoto Mercy Juma
Image caption A ranar Lahadi an yi wasan shafe fuska da launi iri-iri a kasar Kenya wanda suka aro daga wata al'adar kabilar Hindu na kasar Indiya.
Hakkin mallakar hoto Mercy Juma
Image caption Ana watsa wa mutum fenti mai launi iri-iri yayin da yake gudu.
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A rana guda a wani bangare na nahiyar wato a birnin Yamoussoukro na kasar Ivory Coast wata mata ce mai sayar da hula.
Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption A ranar Laraba Sarkin Morocco Mohammed VI ya yi buda baki da Shugaban Faransa Emmanuel Macron a fadarsa da ke a birnin Rabat.
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Har ila yau a ranar Laraba wasu masunta ne ke yin su a gabar teku a garin Benghazi a kasar Libya.
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A ranar Asabar, 'yan wasan Guinea da Ivory Coast gabanin su yi wasan neman tikitin shiga Cin Kofin Afirka, sun nuna alhininsu ga marigayi ,Cheick Tiote, wanda ya rasu a filin wasa a kasar China.
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A ranar Litinin, abokan wasan marigayin na kungiyar Beijing Enterprises sun halarci jana'izarsa...
Hakkin mallakar hoto Alex Duval Smith
Image caption Hakazalika a ranar Alhamis, daruruwan 'yan uwa da abokan arziki ne suka je filin jirgin saman Abidjan don tarbar gawarsa.
Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wani dan sintiri a garin Maiduguri a arewacin Najeriya ranar Juma'a.
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A ranar Alhamis wani dan tasi ne ya rufe wata babbar hanya a lardin Gauteng na Afirka ta Kudu a fafutikar ganin a rage farashin motar Toyota.
Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Har ila yau a ranar Alhamis wannan keken dokin ya je wani gidan mai don a duba lafiyar tayoyinsa a birnin Johannesburg na Afirka ta Kudu.

Labaran BBC