BH: An karkatar da rabin abincin 'yan gudun hijira

Boko Haram Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kayan abinci da aka kai sansanin 'yan gudun hijira dake Bama

Jami'ai a Najeriya sun ce rabin kayan abincin da gwamnati ta aika da su don taimakawa mutanen da rikicin Boko Haram ya shafa, ba su shiga hannun mutanen ba.

Mai magana da yawun Yemi Osinbajo, mukaddashin shugaban kasar, ya ce sabon tsarin da aka bullo da shi a farkon wannan watan, ya taimaka sosai wajen rage karkatar da kayan abincin.

Ya ce yanzu, daruruwan sojoji da 'yan sanda ne ke yi wa kayan abincin rakiya a arewa maso gabashin kasar.

Kimanin mutum miliyan uku ne suka rasa muhallansu sakamakon rikicin na Boko Haram a tsawon shekaru takwas.

Wasu mutanen miliyan daya da rabi kuma na fuskantar barazanar bala'in yunwa.

Mayakan kungiyar ta Boko Haram na ci gaba da kai hare-hare, duk da galabaitar da su da sojojin kasar suka ce sun yi.