Gobarar daji ta halaka mutum 60 a Portugal

portugal fire Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Tun a ranar Asabar gobarar ta ke ci

Daruruwan 'yan kwakwana na ci gaba da fafutukar kashe wata wutar daji a tsakiyar Portugal, wacce ta halaka mutum fiye da sittin.

Akasarin mutanen sun mutune a cikin motocinsu, yayin da suke kokarin ficewa daga gundumar Pedrógão Grande, wacce ke da yawan dazuzzuka.

Da yake jawabi bayan ya ziyarci yankin da gobarar ta tashi, Firayiministan kasar, Antonio Costa ya ce masu kashe gobarar, sun kashe wutar a wurare dari da hamsin a fadin kasar.

Ya sanar da zaman makoki a fadin kasar na kwana uku, sannan ya bayyana al'amarin a matsayin bala'in gobara mafi muni da kasar ta fuskanta a shekarun baya-bayan nan.

An tura sojoji bataliya biyu domin su bayar da taimakon gaggawa.