Harin masallaci a London ya janyo asarar rai

Harin Masallacin Finsbury Hakkin mallakar hoto Reuters

'Yan sandan London sun ce mutun ɗaya ne ya mutu sannan mutum takwas suka jikkata bayan wata motar ɗaukar kaya ta bi ta kan mutanen da ke tafiya a kasa bayan sun fito daga masallacin Finsbury Park da ke arewacin birnin.

Firai Minista Theresa May ta ce harin ya yi kama da na ta'addanci.

'Yan sanda ma sun bayyana shi a matsayin wani "babban lamari".

An tsare mutum daya bayan motar ta kutsa kai a kan mutanen da ke tafiya a kusa da masallacin, wanda ke kusa da kan titin Seven Sisters.

An kira jami'an tsaro da misalin karfe 12:20 na tsakar dare kuma har yanzu suna can, a cewar rundunar 'yan sandan birnin.

Majalisar Musulmin Birtaniya ta ce da gangan babbar motar ta fada kan masu ibada.

An yi amannar cewa akasarin mutanen da lamarin ya rutsa da su sun kammala sallar Isha'i ne bayan sun sha ruwa a lokacin da suke kan hanyarsu zuwa gida.

Hukumar kwana-kwana ta birnin Londonta ce ta aika da ma'aikatanta da dama zuwa wurin.

Tuni jami'an tsaro suka killace wurin.

Wani bidiyo da aka wallafa kan yadda lamarin ya faru ya nuna yadda mutane suka fada cikin rudani a lokacin da ake kokarin taimakawa wadanda suka ji rauni.

Hakkin mallakar hoto EPA
Hakkin mallakar hoto PA

An ga wani mutum yana taimakawa wani mutumi da ya jikkata a kan titi yayin da aka ga wani kuma yana yi wa wani wanda ya samu rauni a kansa magani.

Wani ganau ya ce ya kauce daga kan hanya a lokacin da motar ta kai harin.

Ya kara da cewa: "Mutumin da ke cikin motar ya far mana babu zato babu tsammani. Akwai mutane da dama. An gaya mana mu rika tafiya ba tare da mun kauce daga hanya ba. Na yi matukar kaduwa."

Rashin hankali

Firai Ministar Burtaniya Theresa May ta bayyana harin da cewa: "Wannan mummunan al'amari ne. Ina mika jajena ga mutanen da suka jikkata da 'yan uwansu da kuma masu bayar da agajin gaggawa da suka je wurin".

Shi ma jagoran jam'iyyar Labour Jeremy Corbyn, wanda yake zaune a kusa da wurin da lamarin ya faru, ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa: "Na yi matukar kaduwa da jin labarin harin da aka kai Finsbury Park a dare yau [ Lahadi]. Na yi magana da masallatai da 'yan sanda da kuma hukumar yankin Islington a kan wannan lamari. Ina mika jajena ga al'umar da wannan ibtila'i ya shafa".

Magajin birnin London Sadiq Khan ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa jami'an bayar da agajin gaggawa sun je wurin da lamarin ya faru kuma ana gudanar da bincike kan batun.

Mohammed Shafiq na gidauniyar Ramadhan Foundation, wata kungiyar Musulmi da ke yaki da masu tsattsauran ra'ayi, ya bayyana harin a matsayin "rashin hankali da shaidanci".

Hakkin mallakar hoto Reuters

Labarai masu alaka