Jaririn da ya samu garabasar hawa jirgi iya rayuwarsa

An Indian security official looks on as an aircraft of Jet Airways taxies after landing at Indira Gandhi International Airport in New Delhi on September 12, 2012 Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kamfanin jirgin saman ya ce, wannan ne karo na farko da aka haihu a cikin jirginsu

Wani kamfanin jiragen sama mai zaman kansa, Jet Airways na kasar Indiya, ya yi alkawarin bayar da kyautar tikitin zirga-zirga har karshen rayuwar wani jaririn da aka haifa a cikin jirgin sama mallakin kamfanin. Jirgin ya taso ne daga kasar Saudiyya za shi Indiya.

Ma'aikata da fasinjojin jirgin ne, suka taimaka a lokacin haihuwar jaririn, bayan da nakuda ta ci karfin matar. Haihuwar ta auku ne a kololuwar sararin samaniya mai kimanin tsawon kafa 35,000 daga kasa.

Bayan da jirgin ya sauka, an kai mai jegon da jaririnta asibiti a birnin Mumbai.

Kamfanin jirgin saman ya shaida wa BBC cewa suna cikin koshin lafiya.

Kamfanin ya gode wa ma'aikatansa da Mini Wilson, wacce itace ma'aikaciyar kiwon lafiya da ta karbi haihuwar, a kan kokarin da suka yi "wajen karban haihuwar jaririn cikin nasara".

Kamfanin ya kara da cewa, "wannan ne karo na farko da aka haifi jariri a cikin jirgin saman kamfani yayin da yake tafiya".

Labarai masu alaka