An tsinci gawar wata yarinya a kusa da Masallaci a Virginia

Hoton yarinyar da ta bace bayan harin na jihar Virginia Hakkin mallakar hoto Facebook - Isra Chaker
Image caption Wasu kawayen ta sun tabbatar da hoton yarinyar mai suna Nabra Hussein ne

'Yan sanda a jihar Virginia ta Amurka, sun tsinci gawar wata yarinya musulma mai shekara 17, wacce a kwanakin baya ta bace a kusa da wani masallaci.

'Yan sanda sun ce, matashiyar mai suna Nabra Hussein, na tare da kawayenta a yayin da suka fara 'yar hatsaniya da direban wata mota a Herndon.

Sun ce, mutumin ya fito daga motar, sannan ya far ma yarinyar.

An kama wani mutumin da ake zargi mai shekaru 22 da haihuwa, ana tuhumarsa da laifin kisan kai.

Rahotanni na cewa ana gudanar da bincike ko kisan na nuna kiyayya ne.

Washington Post ta yada wani rahoto da yake cewa, matasa hudu ne ciki har da Nabra suka ziyarci wani gidan cin abinci, inda suka sha ruwa bayan sun kai azuminsu, na watan Ramadan.

Da misalin karfe 8:00 direban motar ya tunkare su a yayin da suke tafiya cikin wani layi.

A lokacin ne wasu mambobin kungiyar Musulmai suka ceci 'yan matan, amma ban da Nabra. Bayan bacewar ta sun sanar da hukumomi lamarin.

Hakkin mallakar hoto Fairfax Police
Image caption A cewar 'yan sanda nan ne wurin da abin ya faru

'Yan sandan sun ce, a lokacin da suke bincike sun tsayar da motar da Darwin Martinez Torres ke tukawa.

Yan sandan sun ce, da misalin karfe 3:00 ne suka tsinci gawar yarinyar a wani wuri mai nisan kilomita biyar daga inda abin ya faru.

Za a binciki hakikanin dalilin mutuwar yarinyar.

Hakkin mallakar hoto Fairfax County Police Department
Image caption Ana tuhumar Darwin Martinez Torres da laifin kisan kai

Mahaifiyar Nabra, Sawsan Gazzar, ta shaida wa jaridar Washington Post cewa, "Ina ganin dalilin da a ka kashe ta na da nasaba da irin kayan da ta sa, da kuma cewa musulma ce,".

Labarai masu alaka

Karin bayani