Nigeria: An kashe mutane a hare-haren Taraba

Nigeria Police Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Rahotanni sun ce duk da cewar an girke jami'an tsaro a garin Ngorouge domin dakile hare-haren, an kai hare-hare a wasu kauyukan da ke kusa da garin.

Rahotanni daga Najeriya na cewa an kashe mutane tare da lalata kadarori da dama a hare-haren da aka kai matsugunan Fulani a karamar hukumar Sardauna da ke jihar Taraba a Arewa Maso Gabashin Najeriya.

Hukumomin Najeriyar dai sun tura jami'an soji zuwa yankin Mambila na jihar Taraba domin dakile rikicin kabilanci da aka kwashe kwanaki biyu ana yi.

Bayanai sun nuna rikicin ya soma ne daga shekaran jiya Asabar zuwa jiya Lahadi a garin Ngorouje da makwabatan kauyukka tsakanin Fulani da Mambila abin da ya kai ga hasarar rayuka.

Rikicin dai ya samo asali ne daga zargin da daya daga cikin kabilun ke yi wa dayar na mai da ita saniyar-ware wajen rabon madafun iko.

Ga karin bayani da Sanata Yusuf Abubakar Yusuf, dan majalisar dattawan da ke wakiltar mazabar Taraba ta tsakiya ya yi wa Haruna Shehu Tangaza:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Karin bayani daga Sanata Yusuf Abubakar Yusuf

Jaridar Daily Trust ta ambato mazauna kauyukan da lamarin ya shafa suna cewa wasu matasa ne suka afka wa kauyukan inda suka kona gidaje kuma suka kashe shanu da yawa.

Labarai masu alaka