Nigeria: Boko Haram ta kashe Mutum 17 a Dalori

Mutum 17 ne suka mutu a harin na Dalori
Image caption Mutum 17 ne suka mutu a harin na Dalori

Rahotanni daga jihar Borno sun ce akalla mutum 17 ne suka mutu a wasu hare-haren kunar bakin wake da aka kai kewayen garin Dalori a jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya.

An kai hare-haren ne ranar Lahadi da daddare a lokacin da jama'a ke shirin komawa gida bayan sallar Asham.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar ta Borno Victor Isuku ya shedawa BBC cewa 'yan kunar bakin wake 5 sun mutu a harin, sai kuma fararen hula 12 da hare-haren suka yi sanadiyyar mutuwarsu.

Ya ce mutane 11 sun jikkata a hare-haren da aka kai kauyen Kofa da ke kusa da Dalori.

Babban jami'in hukumar bada agajin gaggawa, NEMA a shiyyar arewa maso gabas Muhammad Kanar ya ce, biyu daga maharan sun mutu ne a cikin garin Dalori yayin da bama-bamansu suka tashi da su a kan hanya.

Wani da ke sansanin gudun hijira na Dalori 2 ya shedawa BBC cewa, wasu daga maharin sun yi yunkurin shiga sansanin, to amma da ba su yi nasara ba sai suka karasa kauyen Kofa da ke makwabtaka, inda suka tayar da bama-bamansu a cikin jama'a.

Ana dai samun karuwar hare-hare a jihar Borno a 'yan kwanakin nan, duk kuwa da ikirarin karya kashin bayan kungiyar Boko Haram da sojojin Najeriya suke yi.