An bayyana sunan wanda ya kai harin London

Masallaci Hakkin mallakar hoto Getty Images

An bayyana sunan mutumin da ake zargi ya kai harin kan masallata a birnin Landan, sunan mutumin Darren Osborne kuma ya fito ne daga garin Cardiff na Birtaniya.

An kama shi ne bayan da wata mota ta bi ta kan wasu masallata da suke sallar tarawiy a wani masallaci da ke arewacin Landan.

Ana tsare da Mista Osborne (mai shekara 47) ne bisa zarginsa da aikata kisan gilla da kuma aikata laifukan ta'addanci.

'Yan sanda suna ci gaba da bincike a wani gida da ke yankin Cardiff.

Ministar Tsaro Ben Wallace ya ce jami'an tsaro ba su san wanda ake zargin ba a baya, kuma ya yi amannar cewa shi kadai ya aikata laifin.

An yi Allah-wadai da harin

Firai Ministar Birtaniya Theresa May ta ce harin ta'addancin da aka kai kusa da wani masallaci "babban abin takaici ne" kamar sauran hare-hare da suka faru a kasar.

Mutum daya ya mutu yayin da mutane takwas suka jikkata bayan wata motar É—aukar kaya ta bi ta kan mutanen da ke tafiya a kasa bayan sun fito daga masallacin Finsbury Park da ke arewacin birnin Landan.

Ta maimaita kalaman da ta yi bayan harin gadar Landan, inda ta ce "muna yawan kauwar da idonmu a kan masu tsatstsauran akidoji a shekaru masu yawa."

Har ila yau, ta ce babu wani sauran wurin buya ga masu tsatstsauran ra'ayi.

Hakzalika, Shugaban Jam'iyyar adawa ta Labour Jeremy Corbyn ya ce "ya kadu matuka yayin da ya samu labarin harin", kamar yadda ya bayyana a shafinsa na Twitter.

Kwamishiyar 'yan sandan birnin Landan, Cressida Dick, ta ce "a bayyana yake an kai wa Musulmi hari ne ."

Ta ce birnin zai samu karin jami'an tsaro ciki har da wadanda za su rika yin sintiri da makamai "musamman ma a kusa da wuraren ibada".

Wane ne ya kai harin?

Wani mutum ne mai shekara 48 da haihuwa, kuma 'yan sanda sun ce shi ne direban motar daukar kayan da ake zarginsa da aikata kisan gilla.

Jama'a sun kama direban motar gabanin zuwan 'yan sanda.

'Yan sanda sun ce yanzu yana asibiti, amma za su tsare shi da zarar an sallame shi daga asibitin.

Sai dai ba a bayyana sunan mutumin ba tukuna.

Wadanda suka shaida al'amarin sun yi amannar cewa ba mutum guda ba ne kawai yake da hannu a kai harin, amma wata sanarwa da ta fito daga jami'an 'yan sanda ta ce babu sauran wani da suke zargi.

Jami'ai masu bincike kan al'amarin suna binciken motar daukar kayan.

Su waye harin ya rutsa da su?

A ranar Litinin 'yan sanda sun tabbatar da mutuwar mutum daya bayan harin, amma ba a bayyana sunansa ba tukuna.

Mutumin da ya rasun shi ne wanda aka fara ba agajin gaggawa gabanin kai harin.

'Yan sanda sun ce za su yi bincike kan ko ya mutu ne sanadiyyar harin ko kuma daga wani abu na daban.

Jami'an asibiti sun ce mutane tara ne suke bai wa magani a wasu asibitoci uku da ke birnin, inda wasu daga cikinsu suke fama da manyan raunuka.

Hakazalika, an ba wasu da suka ji kananan raunuka magani a wurin da aka kai harin.

Labarai masu alaka