An ƙara wa'adin dokar ta-ɓaci a Nijar

Nijar Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Gwamnatin Nijar ta kafa rundunar musamman don yaƙar masu tada ƙayar baya da ke fitowa daga arewacin Mali

Hukumomi a jamhuriyar Nijar sun kara wa'adin dokar ta-baci da watanni uku a wasu yankunan yammacin ƙasar masu iyaka da ƙasar Mali.

Dokar wadda ta fara aiki a ranar Lahadi, za ta yi tsawon wata uku ne.

Kuma za ta shafi wasu gundumomi ne da ke jihohin Tillaberi da kuma Tahoua.

An kashe sojoji 22 a Jamhuriyar Nijar

An sace wani dan Amurka a Nijar

Nijar: Sace-sace sun addabi Damagaram

'Yan bindiga sun kashe 'yan sanda a jamhuriyar Nijar

Akwai sansanonin jami'an tsaro da kuma na 'yan gudun hijiran kasar Mali a wadannan yankunan.

Kuma a can ne aka fi fama da hare-haren masu tada kasar baya da suke shigo wa daga kasar Mali.

A watan jiya ne Majalisar Dinkin Duniya ta ce an kai hare-haren fiye da 30 a tsawon shekara daya a yankin yammacin Nijar, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar mutune da dama.

Akwai rahoton Baro Arzika daga Nijar kan wannan batun (sai ku latsa alamar lasifika da ke ƙasa don ku saurara)

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Rahoton Baro Arzika kan tsaiwaita dokar ta-ɓaci a wasu yankuna na Nijar

Labarai masu alaka