An fallasa bayanan sirrin Amurkawa kusan miliyan 200

A US flag made out of binary code Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An fallasa bayanan sirrin Amurkawa kusan miliyan 200 a intanet

Wani kamfanin kasuwancin da Jam'iyyar Republican ta dauka aiki ya fallasa bayanan sirrin Amurkawa kusan miliyan 200 bisa kuskure.

Bayanan sun kai yawan terabyte 1.1, kuma sun kunshi kwanan watan haihuwa, da adireshin gida, da lambobi wayar tarho da ra'ayin siyasar kusan kashi 62 cikin dari na dukkan mutanen Amurka.

An ajiye bayanan ne a wani rumbun ajiya na Amazon a intanet.

Duk wanda yake da adireshin rumbun ajiyar na iya shiga yayi abin da ya ga dama da bayanan.

An fallasa ra'ayoyin siyasa

Wani kwararren mai bincike a fannin tsaro na intanet, Chris Vickery ne ya gano wannan katobarar. Da alama an tattara bayanan daga wurare daban-daban ne - kamar shafin intanet na Reddit zuwa bayanan da kwamitocin jam'iyyar Republican mai mulki suka tattara.

A watan Janairun da ya gabata aka shigar da bayanai na karshe, a daidai lokacin da a ka rantsar da shugab Trump.

"Mun dauki alhakin wannan laifin. Bayan binciken da muka gabatar, ba ma ganin an yi mana kutse ne", in ji Alex Lundry shugaban kamfanin Deep Root, a wata ganawa da yayi da Gizmodo.

"Tun da muka ankara da wannan matsalar, mun dauki matakan kare bayanan daga shiga hannayen jama'a ba tare da izini ba".

Ana ganin ban da bayanan, akwai bayanan irin addinin da kowane Ba Amurke ke bi, da jinsinsa da jam'iyyar siyasar da yake mara wa baya, da kuma ra'ayinsa a kan batutuwa kamar ikon daukar bindiga da zubar da ciki.

Abin damuwa

Duk da an dade da sanin cewa jam'iyyun siyasa kan tara bayanan masu kada kuri'a, amma wannan shi ne babbar fallasa da aka taba yi a tarihin Amurka. Masana sun nuna damuwarsu a kan irin abin da wannan batu zai haifar.

"Wannan abin damuwa ne matuka. Ba don an bayyana na sirri ba, a'a, bayanai ne da zasu iya sanar da wanda ya ke so irin tunanin Amurkawa a kan kowane batu", in ji Frederike Kaltheuner na kungiyar Privacy International a wata hira da BBC.

Ya kara da cewa, "Wannan kalubale ne ga demokradiyya. Jam'iyyar Republican ta dogara a kan bayanan da wasu wadanda ba gwamnati ne ba suka tara. Babu wanda zai iya sanin za a yi amfani da bayanan wajen shiga cikin sirrin rayuwarsu kamar haka. Ana iya muzguna masu a siyasance da wadannan bayanan."

Karin bayani