Gwamnatin Gambia ta ce matasa su dawo gida su yi aure

Adama Barror
Image caption Shugaba Adama Barrow ya zama shugaban Gambia bayan zaben da aka yi a kasar mai cike da tarihi

Gwamnatin kasar Gambia ta yi kira ga matasan kasar da ke tafiya ci-rani kasashen waje, su koma gida domin aurar 'yan uwansu mata da suka yi yawa a kasar.

Ministan ma'aikatar yawon bude ido da al'adun kasar Hamat Bah, shi ne ya sanar da hakan, inda ya ce maimakon tafiyar kasadar da suke yi da hadarin da suke fuskanta a cikin sahara, ya kamata su zauna a kasar su domin ancan aka fi bukatarsu.

Ba wai batun hadarin da suke fuskanta ne kadai, dalilin da ya sa gwamnati ta yi wannan kira ba, yawan matan da ba su da aure na daga cikin dalilan da gwamnati ta bayar.

An yi ta sukar kalaman da ministan ya yi, inda wasu ke kafafen yada labaran Gambia suka fara yada cewa Mista Bah ya umarci maza masu mace daya su kara aure daga biyu har zuwa hudu.

An yi ittifaki'in cewa a Gambia sai ka ga mata bakwai, kafin namiji guda ya wuce - hakan ya nuna adadin matan ya rubanya maza da kusan sama da kashi 50 cikin 100.

Mista Hamar Bah ya ce babu inda ya umarci wani namiji ya auri mata hudu,''Na yi wannan kalami ne a wajen wani taron addini da aka gayyace ni, abin da nake nufi shi ne matasan Gambia na sayar da ransu da yin kasadar tsallakawa kasashen turai alhalin 'yan uwansu mata da ke kasar nan ba su da aure''.

''Ban ji dadin yadda aka fassara kalaman da na yi ta wata fuska ba, an min mummunar fahimta. Ai addinin musulunci ya ba mu damar auren mace sama da daya idan da hali har hudu namiji zai iya aura'', in ji Mista Bah.

Da aka tambaye shi ko me ya ja hankalinsa har ya yi wannan kira, sai ya kada baki ya ce ''Gaskiya mata sun fi maza yawa a kasar nan, musamman tsakanin matasa, gida bai koshi ba ai ba a kai wa dawa ba''.

Labarai masu alaka