Jose Mourinho na fuskantar tuhumar zamba a Spain

Mouhinho Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mourinho ya jagoranci Madrid daga shekarar 2010 zuwa 2013

Hukumomi a kasar Spain suna tuhumar kocin kulob din Manchester United, Jose Mourinho, bisa zambar haraji a lokacin da yake kocin kulob din Real Madrid.

Masu shigar da kara na tuhumar kocin da zambatar kasar Spain euro miliyan 3.3 (wato kimanin dala miliyan 3.6) na kudin haraji tsakanin shekarun 2011 zuwa 2012.

Kawo yanzu Mourinho bai ce uffan ba tukuna.

A kwanakin baya ne hukumomin kasar Spain suka tuhumi wasu manyan 'yan wasan kwallon kafa da zambar haraji.

Ciki har da dan wasan Barcelona Lionel Messi, wanda a halin yanzu ke fuskantar zaman kaso na watanni 21 da kuma Cristiano Ronaldo na Madrid da sauransu.

Labarai masu alaka

Karin bayani