Algeria: Kotu ta daure uban da ya zuro dansa ta tagar bene

Facebook Hakkin mallakar hoto Al Arabia
Image caption Hoton da mutumin ya dauka a domin samun karin masoya a Facebook

Wata kotu dake birnin Algiers ta yanke wa wani mutum hukuncin daurin shekara biyu a gidan kaso, sabo da zuro dansa daga wata tagar bene yana lili, domin ya sami karuwar masu son abubuwan da yake wallafawa a shafinsa na Facebook.

Mutumin ya wallafa hoton bidiyon a shafinsa na Facebook a yayin da yake rike da yaron da hannu daya ta tagar wani dogon bene mai hawa 15. Kuma ya bukaci: 'A bani "Like" 1,000, ko in sake shi'.

Wannan ya sa ma'abota shafin na zumunta suka ringa kiraye-kirayen a hukunta shi da laifin cin zarafin yaron, bayan da suka kalli bidiyon aika-aikar.

Yaron ya firgita sosai domin abin da mahaifin nasa yayi.

Da alama dai mutumin yayi wannan abin ne domin samun karin masoya a shafinsa na Facebook.

Image caption Michael Jackson ma ya taba yin irin wannan gangancin a shekara ta 2002

A shekarar 2002 mawaki Michael Jackson ma ya aikata irin wannan gangancin da dansa daga tagar hawa na uku na otel din da ya sauka.

Marigayin ya jawo kace-nace yayin da ya rike yaron ta tagar dake birnin Berlin na kasar Jamus; amma daga baya ya nuna jimaminsa game da lamarin.