Yara Amurkawa 1,300 ne ke mutuwa ta hanyar harbin bindiga

Masu zanga-zanga a Amurka Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Masu adawa da tashin hankalin da bindiga ke janyowa a wajen ofishin kungiyar masu bindigogi a birnin Washington DC

Wani bincike na gwamnati ya gano cewa kimanin yara 1,300 ne da shekarunsu basu haura 17 ba ke mutuwa a sakamakon harbi bindiga a Amurka.

Masu bincike na cibiyar hana yaduwar cututtuka da ke Amurka sun kuma gano cewa yara 5,800 ne ke samun munanan raunuka daga harbin bindiga a duk shekara.

Maza ne kashi 82 cikin dari na yaran da ke mutuwar, yayin da kuma akwai yiwuwar sau goma za a kashe bakaken fata da bindiga, a cewar binciken.

Haka zalika fiye da rabin mutuwar kashe su ake yi, yayin da kuma kashi 38 cikin dari sun kashe kansu ne.

Sakamakon binciken wanda aka wallafa a ranar Litinin, ya kuma gano cewa kashi shida cikin dari na mutuwar sun faru ne a sanadiyyar raunukan da aka samu na harbi bisa kuskure.

Katherine Fowler wadda ta jagoranci binciken ta ce "Raunukan da ake samu ta hanyar harbin bindiga su ne suka fi janyo mutuwar yara daga shekara daya zuwa masu shekaru 17 a Amurka a duk shekara. Haka kuma suna matukar janyo rashin lafiya da kuma nakasa ga yara."

Maharin da ya far wa 'yan Majalisar Amurka ya mutu

Wasu mutane sun kai ƙorafi caji ofis riƙe da bindiga

Dan bindiga ya harbe mutum biyar a Florida

"Yara 19 ne ke mutuwa a rana ko kuma ake kula da su a sashen kula da marasa lafiya na gaggawa, sakamakon raunukan harbin bindiga a Amurka." Katherine ta shaida wa kamfanin dillacin labarai na Reuters.

Binciken ya kuma gano cewa an samu karuwar kashe kai da bindiga da kashi 60 cikin dari daga shekarar 2007 zuwa shekarar 2015, a cewar sharhin da aka yi bisa bayanan raunuka na kasa.

Akwai yiwuwar da ta kai har sau hudu zuwa biyar cewa 'ya'yan Turawa da kuma 'yan asalin Amurka za su iya kashe kansu da bindiga.

An fi samun kisan kai ta hanyar harbi bisa kuskure a lokacin da yara ke wasa da bindiga.

Binciken dai na zuwa ne bayan wani yaro dan shekara hudu a jihar Pennsylvania ya harbi fuskarsa ya mutu a ranar Lahadin da ta gabata.

'Yan sanda a karamar hukumar Monroe ba su gurfanar da kowa dangane da hakan ba.

Mahaifiyar yaron mai shekari 21, Lexie Antonini, ta ce ta shiga wani yanayi.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Yara kan yi wasa da bindigar mahaifansu, abin da a wani lokaci su kan yi harbi bisa kuskure

Lexie ta rubuta a shafinta na Facebook cewa "Ban taba tsammanin zan ga ranar da zan ji labarin mutuwar dana ba, dana tilo ya rasu .....dan yaro na."

"Ba zan iya bayyana yadda nake ji ba. Ban san me zan yi ba. Na rasa komai."

Binciken cibiyar ya kuma duba yadda lamarin matuwar yaran ta hanyar harbin bindiga ta ke a matakin jihohi, inda ta gano cewa gundumar Columbia da Louisiana sun fi kowanne yawan irin wadannan mace-macen.

Sai Delaware da Hawaii da Maine da kuma New Hampshire wanda aka samu mutuwa 20 ko kasa da haka, a cewar binciken.

Masu binciken kuma sun yi nuni da cewa da wuya ake samun yara sun samu rauni ko kuma mutuwa a sanadin bindiga a wasu kasashen da suka ci gaba.

Asali ma fiye da kashi 90 cikin dari na yara 'yan shekaru 14 zuwa sama da haka a wasu kasashen masu arziki, suna zaune ne a Amurka.

Labarai masu alaka