Kamaru: Tsananin zafi yasa mutane rufin jinka

Gida mai rufin jinka Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An samun gidaje masu rufin jinka a yankunan karkara a kasashen Afrika

Sakamakon tsananin zafin da ake yi a yankin arewacin Kamaru ya sa mutane sun rungumi hanyar rufin daki da ciyawa.

Matsalar ta kara kamari ne saboda karancin wutar lantarki da zai ba wa jama'a damar sanyaya dakuna da na'urori na zamani.

Hakan ya sa wasu suka koma wa rufin dakuna da jinka wadda ake yi da busasshiyar ciyawa.

Yin amfani da jinkar na bai wa jama'a samun kariya daga zafin rana da kuma kura.

Wani wanda ke sakar jinkar, Nura Isyaku ya ce rufin na daukar shekaru kimanin biyar kafin ka sake jinkar.

Inda ya kara da cewa rufin jinkar kan hana jin karar zubar ruwan sama a kan rufin kwano.

Wani magidanci ya bayyana cewa rufin jinkar na taimaka wa mutane su samu bacci da daddare saboda zafi ba zai dame su ba.

Labarai masu alaka