Allurar rigakafin ciwon TB ta ƙare a Nigeria

Rigakafi Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Tarin fuka yana daya daga cikin manyan cututtukan da ke kashe yara a duniya

Allurar rigakafin tarin fuka wato TB da ake wa jarirai sabbin haihuwa ta kare a asibitotin Najeriya, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Cutar tana daya daga cikin cututtukan da ake wa yara allurar rigakafinsu, saboda yadda take daya daga cikin mayan cututtukan da ke saurin kashe su.

Dokta Hassan Muhammad Garba wanda shi ne shugaban kungiyoyin daraktocin asibitoci masu zaman kansa a Najeriya reshen jihar Bauchi, ya ce allurar ta kare gaba daya a fadin kasar.

Har ila yau, ya ce suna sayen allurar ne "daga hannun gwamnati don ba a samun ta a kasuwa."

Ya ce yanzu kimanin wata guda ke nan da fara fuskantar karancin allurar.

Sai dai ba mu samu damar jin ta bakin jami'an kiwon lafiyar Najeriya ba tukuna.

Ga karin bayanin Dokta Hassan Muhammad Garba kan matsalar (sai ku latsa alamar lasifika da ke ƙasa don ku saurara)

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Dokta Hassan Muhammad Garba yana bayani kan matsalar karancin allurar a kasar

Labarai masu alaka