Saudiyya ta kori raƙuman Qatar daga kasarta

Rakuma Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Akwai 'yan Qatar da dama da suke kiwon rakumansu a Saudiyya saboda kasarsu ba ta da isashen abincin dabbobi

Saudiyya ta ce wajibi ne raƙuma da tumakai mallakar kasar Qatar da suke amfani da filayen kiwonta su fice daga kasar, a ci gaba da takaddamar da ke ruruwa tsakanin Qatar da sauran kasashen Larabawa.

Qatar ta ce akalla rakuma 15,000 da tumakai 10,000 ne suka shiga iyakar Saudiyya don kiwo.

Sai dai ta ce an kafa wani sansanin wucin gadi a Qatar wanda ya tanadi harawa da kuma tankunan ruwa don dabbobin da aka koro.

Akwai 'yan Qatar da dama da suke kiwon rakumansu a Saudiyya saboda kasarsu ba ta isashen abincin dabbobi.

A farkon watan nan ne kasar Saudiyya da wasu kasashen Larabawa suka yanke hulda da kasar Qatar bisa zargin kasar na goyon bayan ta'addanci.

Qatar ta musanta zargin.

Ma'aikatar muhalli ta Qatar ta ce sansanin wucin gadin zai ci gaba da kulawa da dabbobin har sai bayan an kammala aikin sabo na dindindin.

Har ila yau, ma'aikatar ta ce ta tura masana kan lafiyar dabbobi da sauran jami'ai zuwa wurin don kulawa da dabbobin.

Wani jami'in a Qatar ya ce dabbobi 25,000 aka dawo da su kasar, kamar yadda ya bayyana wa shafin intanet na jaridar al-Raya.

Wadansu faya-fayan bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta sun nuna lokacin da garken rakuman ke ketarawa zuwa cikin kasar Qatar daga Saudiyya.

Labarai masu alaka