Dan kunar baƙin wake ya tashi bam a tashar jirgin Belgium

Sojojin kasar Belgium a bakin aiki
Image caption Jami'an tsaro na taimakawa mutane ficewa daga tashar jirgin kasar

Sojoji a Belgium sun harbe dan kunar bakin waken da ya kai hari tashar jirgin kasar birnin Brussels.

'Yan sanda sun ce dan kunar bakin wake na sanye da wata shimi da ake zaton bama-bamai ne a kasan ta, inda ya tashi abin da ke jikinsa, kuma nan take sojojin suka harbe shi.

Mai magana da yawun 'yan sandan Brussels ya bayyana mutumin da mai tsattsauran ra'ayi, kuma harin ta'addanci ne da babu wani mutum da lamarin ya rutsa da shi.

Shi ma kakakin ofishin mai shigar da kara na kwamnati Eric Van Der Sypt, ya ce kawo yanzu ba a tabbatar ko maharin ya na raye ko ya mutu ba.

Tuni jami'an tsaro suka killacebabbar tashar jirgin, wadda ke cika makil saboda baki 'yan kasashen waje da ke zuwa yawon bude ido.

Mutane sun shiga firgici a lokacin da damarar jikinsa ta tashi, amma daga bisani komai ya lafa bayan zuwan jami'an tsaro.

Tuna shekarar da ta gabata ne aka sanya jami'an tsaro masu sunturi a muhimman wuraren kasar, bayan harin bam mafi muni da ka kai cikin dandazon jama'a.

Labarai masu alaka