An sanya dokar hana fita a Taraba

An kone gidaje da dama a Taraba Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An kone gidaje da dama a Taraba

Hukumomi a Najeriya sun sanya dokar hana fita a jihar Taraba da ke arewa maso gabashin kasar sakamakon rikicin da ya barke tsakanin Fulani da 'yan kabilar Mabila.

Rikicin, wanda ya barke tun a karshen makon jiya a karamar hukumar Sardauna, ya yi sanadin mutuwar mutane da dama.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar ASP David Misal ya shaida wa BBC cewa akalla mutum biyar ne suka mutu sanadiyar rikicin.

Ya ce sun dauki matakin dokar hana fita ne domin kwantar da tarzoma.

Bayanai sun nuna cewa rikicin ya samo asali ne bayan da manoman kabilar Mambila da ke zaune a garin Ngoroje sun yi yunkurin karbar wasu gonaki da filaye da ke hannun Fulanin garin domin su yi noma, lamarin da ya haifar da takaddama tsakanin bangarorin biyu har ta kai ga zuwa kotu.

Rahotanni sun ce daga karshe kotun ta mallaka wa fulani filayen, lamarin da ya sa 'yan kabilar mambila ba su ji dadi ba kuma suka dirar wa fulanin, ko da yake babu wata majiya daga bangaren mambilawan da ta tabbatar da hakan.

Sai dai wasu rahotannin sun ce lamarin ya faru ne sakamakon nuna son kai da aka yi a wurin rabon mukaman siyasa.

Labarai masu alaka