Rikici ya sake barkewa a Jamhuriyar Tsakiyar Afirka

A woman and a child walk past UN peacekeepers from Gabon patrolling the Central African Republic town of Bria on June 12, 2017 Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Rundunar wanzar da tsaro ta majalisar dinkin duniya na sanya ido a Bria

An kashe akalla mutum 40 a rikicin da ya barke a Jamhuriyar Tsakiyar Afirka, kwana guda bayan an sanya hannu kan yarjejeniyar tsagaita bude wuta tsakanin gwamnati da 'yan tawaye.

Magajin garin Bria, arewa maso gabashin birnin Bangui, ya ce an ga gawarwakin mutane yashe a kan tituna.

Yarjejeniyar, wacce aka sanya wa hannu a Rome ranar Litinin, ta bukaci a tsagaita bude wuta nan take.

Ta so ta sanya kungiyoyin masu tayar da kayar baya cikin harkokin siyasa inda su kuma za su ajiye makamansu.

An kashe dubban mutane yayin da aka raba wasu dubban daga muhallansu tunda aka soma fada tsakanin mayakan Musulmi na Seleka da takwarorinsu na Antibakala bayan hambarar da Shugaba Francois Bozize a 2013.

Kungiyaragaji ta Medecins Sans Frontieres ta ce fadan ya kaure ne a Bria da safiyar Talata.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Al'umar Kotolika ta Sant' Egidio ta shige gaba wajen yarjejeniyar

Magajin garin Maurice Belikoussou ya shaida wa kamfanin dillacin labarai na Reuters cewa an kai gawar mutum 42 asibiti.

"Akwai wasu gawarwakin a makwabtanmu wadanda har yanzu ba a kwashe ba," in ji shi.

Kungiyoyin 'yan tawaye da dama ne suka amince su ajiye makamansu nan take bayan an kafa hukumar gano gaskiya da yin sulhu.

Amma masu sharhi sun ce akwai kungiyoyi da dama da ba su nuna sha'awar ajiye makaman ba.

Karin bayani