Ana bikin cin naman kare a yankin Yulin da ke China

An dauki wannan hoton a bara a watan Mayu 9, 2016 Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Tun shekaru 500 da suka wuce ne dai akafa fara al'adar cin kare a kasar

An fara wani bikin cin naman kare a birnin Yulin da ke kasar Sin, duk da rahotannin da aka fitar da fari cewa an soke bikin na wannan shekarar.

An dai saba yin irin wannan bikin ne duk shekara a birnin da ke lardin Guangxi.

A farkon wannan shekarar ne wasu masu fafutuka da ke adawa a Amurka suka yi ikirarin cewa hukumomi sun hana sayar da naman kare.

Sai dai masu sayar da naman sun shaida wa BBC cewa basu da masaniya game da hakan.

Haka kuma a ranar 15 ga watan Mayu jami'ai a birnin sun tabbatar da cewa ba a yi wannan haramcin ba.

Ko ana sayar da naman kare har yanzu?

Rahotanni daga Yulin a ranar Laraba sun bayyana cewa an rarrataye karnukan da aka kyafe a shaguna a kasuwar Dongkou mafi girma a birnin.

Haka kuma akwai rahotannin da ke nuna cewa an baza jami'an tsaro a kan tituna.

Wata mai fafutuka a birnin ta shaida wa BBC cewa 'yan sanda sun hana ta shiga kasuwar Dashichang, inda ta yi imanin ana sayar da karnuka masu rai.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Al'adar cin naman kare na janyo cece-kuce a China

A shekarun da suka wuce an dan samu hatsaniya a lokaci da masu fafutukar kawo karshen al'adar suka yi kokarin kwace karnukan da ake shirin yankawa.

A birnin na Yulin ne aka fi samun masu cin naman kare a lardin na Guangxi.

Sai dai hakan bai samu jan hankalin duniya ba, sai a shekaru goma da suka wuce.

Shin cin naman kare yana da aibu?

Duk batun na hana azabtar da dabbobi ne da kuma sauyi kan yadda Sinawa ke kallon karnuka.

Mazauna birnin da kuma masu sayar da naman karen na cewa, suna kashe karukan ne ba tare da sun wahalar da su ba, kuma cin naman ba shi da wani bambanci da cin naman alade ko akuya ko kuma kaza.

An kwashe shekaru ana wannan al'adar ta cin naman kare a kasashen China da Koriya ta Kudu da wasu kasashen da ke yakin Asiya.

Wadanda ke son wannan al'adar ba sa jin dadin abin da suke yi wa kallon katsalandan da baki ke yiwa al'adu na cikin gida.

Cin naman kare a al'adar Sinawa na da amfani a lokacin bazara.

Har wadanda ma ba sa cin naman karen suna kare al'adar, matukar ba sato karnukan aka yi ba, ko kuma an azabtar da su wajen kashe su.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Yadda yawan masu ajiye kare a gida ke karuwa haka adawa da al'adar ke ci gaba

Amma masu suka na cewa ana cunkusa karnuka a cikin keji idan za a kawo su daga wasu birane saboda bikin, kuma ana azaftar da su yayin kashe su.

Masu fafutukar na kuma zargin cewa an sato karnukan ne.

An yi zanga-zanga a ciki da wajen kasar kuma yawan masu ajiye kare a gida ya karu matuka, inda a shekarun baya-bayan nan suka kai miliyan 62.

Kuma hakan na tasiri wajen sauya ra'ayin masu cin kare.

Me ya kawo rudani a bana?

A watan Mayu, wasu masu fafutuka da ke Amurka sun yi ikirarin cewa an haramta sayar da naman kare a bana. Sai dai ba haka batun yake ba.

Amma hukumomin birnin Yulin sun nanata cewa, ba su suka shirya bikin a hukumance ba, saboda haka ba za su haramta shi ba. Cin naman kare dai ba laifi ba ne a China.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Hukumomin birnin ba su ji dadin kagen haramcin da aka yi ba

Hukumomi a birnin ba su ji dadin yadda kafafen yada labarai ke yayata bikin na bana ba.

A shekarar 2016, sun hana a yanka karnukan a bainar jama'a saboda tunanin cewa za a yi bore.

A bana ma dai ba a yi yankan sosai a bainar jama'a ba, ko da yake ba a kammala bikin ba tukuna.

Masu fafutuka sun kiyasta cewa a wasu shekarun a lokacin bikin ana kashe karnuka da maguna kusan 10,000 kuma a cinye a bikin na kwana goma.