Sarkin Saudiyya ya nada dansa a matsayin yarima mai jiran gado

Prince Mohammed bin Salman (left) and prince Mohammed bin Nayef Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Yarima Mohammed bin Salman (A hagu) ya maye gurbin yarima Mohammed bin Nayef (A dama) a matsayin yarim amai jiran gado

Sarkin Saudiyya ya nada dansa, Mohammed bin Salman a matsayin yarima mai jiran gado, bayan ya cire dan dan uwansa, Mohammed bin Nayef, daga matsayin.

Har ila yau sarki Salman ya ba da umarnin cewa dansa yarima Mohammed mai shekara 31, zai zama mataimakin Firai Minista, yayin da zai ci gaba da rike mukaminsa na ministan tsaro.

An cire yarima Mohammed bin Nayef, mai shekara 57 ne daga mukaminsa na shugaban tsaro na cikin gida, in ji kafafan yada labarai mallakar gwamnati.

Kamfanin dillancin labaran SPA ya ruwaito cewa Nayef ya yi mubaya'a ga sabon yarima mai jiran gadon.

Muhimmancin wannan sauyin

Wadanda suke mulkin kasar dai mutane ne masu shekaru tsakanin 70 zuwa 80.

Amma sanya yarima Mohammed a matsayin mai jiran gado zai sa matasan kasar su fara kallon cewa abubuwa na sauyawa.

kafin samun mukaminsa na baya-bayan nan, yariman ne ya jagoranci yakin Saudiyya a Yemen, yayin da yake lura da manufar masarautar kan makamashi da sauye-sauyen tattalin arziki.

Editan BBC na Gabas ta Tsakiya, Jeremy Bowen, ya ce mai yiwuwa ne yariman ya bata wa wasu rai daga cikin 'yan gidan sarauta wadanda suka saba da jagorancin tsofaffi.

Babansa, sarki Salman yana da shekaru 81, kuma rahotanni sun ce ba shi da cikakkiyar lafiya, in ji wakilin BBC.

Mohammed bin Nayef zai iya shafe gomman shekaru yana jagorancin kasar.


Wa nene sabon yarima mai jiran gado?---Wakilin BBC kan harkar tsaro Frank Gardner

Ci gaban da yarima Mohammed bin Salman ya samu a fagen siyasa abu ne da ya faru cikin kankanin lokaci.

Da Franc ya hadu da shi a Jeddah a shekarar 2013 ya bayyana kanshi a matsayin lauya ne kawai. Amma yau yana gaf da rike mulkin kasa mafi karfi a yankin larabawa.

Duk da cewar shi ne ke jagonrantar yakin Saudiyya a Yemen da ake ta barna wanda kuma yaki ci yaki cinyewa, yana da farin jini a cikin gida, musamman tsakanin matasan Saudiyya.

Ya kori da yawa daga cikin 'yan amshin shata daga aikin gwamanti, kuma ya maye gurbinsu da matasa masu ilimin boko. Ya kaddamar da wani shirin ci gaba mai suna "Vision2030", kuma ya bayyana shirin sayar da wani bangare na katafaren kamfanin man kasar, Aramco.

Ya kuma kulla alaka da Washington da kuma gwamantin Trump.

Amman mataki mafi hatsari ka iya zama kokarinsa na rage ikon malaman addini masu ra'yin 'yan mazan jiya. Washington tana son wannan yunkurin, amman wasu a cikin gida ba sa son hakan.


Yaya ake gadon sarauta a Saudiyya?

Mutumin da ya assasa masarautar, Sarki Abdulaziz (da aka fi sani da Ibn Saud), ya haifi gomman yara, kuma 'yan gidan sarautar kasar sun kai 15,000.

A shekarar 2006, an ayyana wata doka wadda ta nada wani kwamiti da ke da alhakin zaben sarki da yarima mai jiran gado.

Kwamitin ya kunshi manyan mazaje 'yan gidan sarautan Al Saud, kuma an fi sanin kwamitin ne da sunan majalisar mubaya'a.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Mohammed bin Nayef (A dama) ya yi mubaya'a ga Mohammed bin Salman (A hagu), wanda tsuguna kuma ya sumbaci hannunsa.

Labarai masu alaka