Kotu ta umarci gwamnati ta biya diyyar rushe gidaje

Shanty Town Hakkin mallakar hoto By Paolo Black
Image caption Gidajen marasa galihu na gabar teku dake Legas a Najeriya

Wata babbar kotu a Legas, babban birnin kasuwanci na Najeriya ta yanke hukunci a kan shari'ar da fiye da mutane 30,000 suka shigar game da rushe gidajensu da gwamnati ta yi.

Gwamnatin jihar Legas dake kudu maso yammacin Najeriya ta tashi unguwar marasa galihu ta Otodo Gbame daga watan Nuwambar 2016 zuwa watan Fabrairun bana.

Gwamnatin ta ce yankin, wanda yana gabar teku ne, "mai hatsari ne ga muhalli".

Jama'a da dama ne suka hallarci zaman kotun, kuma sun nuna farin cikinsu yayin da alkalin kotun ya yanke hukunci.

Suna ganin wannan babbar nasara ce a garesu.

Kotun ta umarci gwamnatin ta da ta biya diyya ga mazauna unguwar, kuma bangarorin su nemi hanyoyin sasantawa.

Alkalin ya ce an taka hakkokin al'umomin dake zaune a wurin, sabili da rushe muhallansu da gwamnatin tayi, ba tare da ta samar wa wadanda lamarin ya shafa wasu matsugunan ba.

Da farko gwamnatin ta musanta cewa ita ce ta rusa muhallan dake unguwar, inda take ikirarin gobara ce ta ci gidajen.

Ta kuma bayyana cewa ta karasa rushe sauran gidajen a watan Fabrairu ne saboda ta hana bazuwar gobarar.

Ana ganin rushe unguwar Otodo Gbame na cikin tsarin tsabtace yankunan da suke gabar teku, inda mutanen kimanin 300,000 ke zaune.

Gwamnatin jihar Legas bata ce uffan ba game da wannan hukuncin, amma a shekarun baya ta rika yin biris da irin wannan hukuncin.