An kai tsegumin Sarauniyar Ingila wajen 'yan sanda

Queen Elizabeth
Bayanan hoto,

Sarauniyar tana tafiya ne zuwa Westminster tare da Yarima Charles

An kai rahoton Sarauniyar Ingila ga 'Yan sandan West Yorkshire saboda rashin sanya maɗauri a cikin motar masarauta a kan hanyarta ta zuwa bikin buɗe zaman Majalisa.

Wani mutum ne ya buga lambar kar-ta-kwana ta 999, inda ya tsegunta wa 'yan sanda cewa Sarauniya ba ta sa bel ba a motar da ake tuƙa ta a London.

Rundunar 'yan sandan West Yorkshire dai ta tabbatar da cewa lallai wani ya buga waya kuma ya tsegunta mata wannan labari a wani saƙon Twitter.

Asalin hoton, WYP/TWITTER

Bayanan hoto,

Rundunar 'yan sandan West Yorkshire ta ce sau da dama ana kiran lambar 999 kan abubuwan da ba na gaggawa ba

Sai dai a ƙarƙashin dokar Burtaniya, ba za a iya tuhumar Sarauniya, da aikata babban laifi ko na ƙeta dokokin zaman jama'a ba.

Sarauniyar tana tafiya ne zuwa Westminster tare da Yarima Charles don buɗe shekarar Majalisa a hukumance.

Ofishin harkokin yaɗa labaranta, ya ce ba zai mayar da martani kan saƙon na Twitter ba.

Tom Donohoe, na rundunar 'yan sandan West Yorkshire ya ce sau da dama a kan kira layin kar-ta-kwana na 999 ga harkokin da ba na gaggawa ba.

"Mun sha nanata cewa lambar 999 ta kiran gaggawa ce kaɗai," in ji shi, ya kuma ce rundunar aƙalla ba akasara ba tana karɓar kiran gaggawa fiye da 1,000 a rana.

A baya rundunar ta taɓa wallafa jerin kiraye-kirayen lambar 999 da aka ɓata wa 'yan sanda lokaci, ciki har da wani ƙuda da ya shiga ɗakin kwanan wasu da wani ɓera da ke shige da fice.

Game da dokar sanya maɗaurin zama a mota kuwa, shafin intanet na gwamnati ya ce: "Dole ne mutum ya sa maɗaurin zama a mota, matuƙar akwai shi a mazaunin da mutum ke amfani da shi."

Ya ƙara da cewa ana iya cin ka tarar fam 500 saboda rashin yin haka, ko da yake, an yi togaciya kan direbobin da ke tafiya da baya-da baya ko kuma motar da 'yan sanda ke amfani da ita da ta jami'an kashe gobara da ta ma'aikatan ceto.

Shafin Masarautar Ingila ya ce "Sarauniya tana taka-tsantsan don tabbatar da ganin ta gudanar da duk harkokin ƙashin kanta bisa tanadin doka sau da ƙafa".