Kenya za ta raba wa 'yan makaranta audugar mata

Yan makaranta 'yan kabilar Masai na daukar darasi a cikin aji Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Duk 'yan matan da ke zuwa makaranta a fadin kasar ta Kenya ne za a rabawa audugar mata kyauta

Gwamnatin Kenya ta ce za ta raba audugar mata kyauta ga 'yan mata 'yan makaranta saboda su daina fashin makaranta.

Ana fatan wannan yunkuri zai karfafa zuwa makaranta, a kasar da audugar mata ke da dan-karen tsada.

An yi kiyasin cewa tsadar audugar ta janyo mata miliyan daya suna fashin makaranta har na tsawon makonni shida a duk shekara.

Amma a yanzu nauyin ya rataya a wuyan gwamnati ta samar da audugar kyauta ga kowace 'yar makaranta.

Wata sabuwar doka a kan ilimi da shugaba Uhurru Kenyatta ya sanyawa hannu a wannan makon ta ce "dole a samar da auduga tsaftatacciya mai inganci kuma wadatacciya ga dukkanin 'yan matan da aka yi wa rajista a makaranta. Kuma dole a samar da wurin zuba audugar bayan an yi amfani da ita don tsaftace muhalli."

Hakan dai na zuwa ne bayan shekaru goma da cire haraji a kan audugar mata duk don a saukaka farashinta.

Sai dai duk da haka kashi 65 cikin dari na mata da 'yan mata suna ganin tsadar audugar, a cewar wani rahoton da wani kamfani FSG ya fitar a shekarar 2016.

Saboda haka ne ma wata gidauniya da ake kira ZanaAfrica, ke raba audugar mata kyauta ga 'yan mata a fadin kasar.

Matsalar tsadar audugar da kuma tasirin hakan a kan karatun 'yan mata bata tsaya kadai a kasar ta Kenya ba.

A cewar wata kungiya, Point period Campaign 'yan mata na fashin makaranta ma a kasashen India da Nepal da Afghanistan da Saliyo saboda irin wadannan dalilai.

Batun bai ya tsaya kawai a kasashe masu tasowa ba.

An nemi wata kungiya, Freedom4Girls - wadda ke samar da audugar mata ga 'yan mata a Kenya, ta taimaka wa makarantun da ke yankin a arewacin Ingila saboda suna fashin makaranta.

Wata matashiya ta shaida wa shirin BBC na turanci BBC Radio Leeds cewa tana "kunshe safa ne a cikin kanfe" saboda ta samu ta je makaranta.

Karin bayani