'Na dauka zan mutu a Libya': Sai da na biya kudin fansa aka sake ni

Seun pictured near his home in the slums of Lagos, Nigeria
Image caption Bayan dawowarsa Najeriya, Seun yace ya yi nadamar kokarin tafiya Turai

Ana kiransa "Shayin safe" - wani mummunan dukan da akan yi wa 'yan ci-rani da robar ban ruwa. kawai

Seun Femi ya sha irin wannan dukan a kowace safiya har na tsawon wata hudu a hannun masu garkuwa da shi na wani gidan kaso dake Libya.

"Su kan bugi kaina, da hannayena, da duwawuna", in ji Seun, dan shekara 34 da haihuwa. "Mai tsarona kan dake ni har sai ya gaji."

Yatsun Seun guda biyu sun karye a yayin wannan muguwar ukubar da aka gana masa, Amma ya ce ya yi sa'a, domin a gabansa aka yi ta dukan wani har sai da ya mutu.

"Na dauka mutuwa zan yi", in ji shi.

Seun na daka cikin dubban 'yan yankin Afirka ta yamma da ke ratsa hamadar Sahara, suna shiga Libya a kowace shekara, domin a yi fasa kwaurin su zuwa nahiyar Turai a jiragen ruwa.

Tafiya mai matukar hatsari

Hukumar kasa da kasa mai lura da 'yan ci-rani (IOM) ta kiyasta cewa akwai mutanen da yawansu ya kai miliyan daya a cikin Libya suna neman damar tsallaka tekun Bahar Rum.

Tafiya ce mai tsananin wahala, amma yanzu batun ya dauki wani sabon salo, domin 'yan ci-ranin sun zama abin farauta a hannun kungiyoyin mayaka da masu aikata manyan laifuka a Libya, kasar da yaki ya daidaita ta.

Image caption Taswirar hanyoyin da 'yan cirani daga sassan Afirka ke bi a hanyarsu ta zuwa Turai

A farkon wannan shekarar, hukumar ta IOM ta fitar da wani rahoto dake nuna yadda ake sayar da 'yan ci-ranin a "kasuwannin bayi" dake birnin Sabha a kudu maso yammacin Libya.

Seun yace a wannan birnin ne aka tsare shi tare da wasu 'yan ci-ranin kimanin 300 har sai sun biya kudin fansa kafin a sake su.

"Mun dauka masu fasa kwaurin sun kai mu wani wurin da zamu huta ne, amma sai suka tsare mu", in ji shi.

Seun yace wani dan kasar Libya mai kusumbi ne yake shugabancin gidan kason.


Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Irin jirgin ruwan 'yan ci-rani a kusa da gabar teku daga Libya

Gidan kason wani gini ne da ba'a gama gina shi ba. An raba 'yan ci-ranin mazaje gida-gida a dakunan da ake kira 'Ghetto'. Yawancin 'yan ciranin 'yan asalin kasashen Najeriya, da Ghana da Senegal ne. An tsare Seun a 'ghetton' 'yan Najeriya ne.

Akwai ghetto biyu masu suna Ghana da VIP (na manyan mutane), inda masu gadin sukan nemi a biya su kudin fansa mai yawa kafin a sake su.

"Ana hada mu kamar kifin gwangwani a lokacin barci."

Ga kuma karancin abinci, abin da suke da wadatarsa shi ne ruwan sha na roba, domin 'yan ci-ranin na iya mutuwa daga matsanancin kishin ruwa a yanayi mai zafi na Libya.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An kiyasta akwai 'yan cirani miliyan daya dake neman shiga Turai daga Libya.

Tsarin rashin imanin da masu tsaronsu ke yi in ji Seun, shi ne mai tsaronsu kamar wani mai suna "Rambo" na dukan 'yan ciranin, kana ya mika masu wayar hannnu.

"Su kan bamu damar kiran 'yan uwanmu sau daya a kowane yini", in ji shi. "Sai su rika dukanmu a lokacin da muke magana da 'yan uwan namu, saboda su san halin da muke ciki. Mu kuma sai mu roke su su aiko mana da kudi."

A ranar Talatar da ta gabata, jami'an kasar Italiya sun ce sun kama wani mai suna "Rambo", wanda yayi suna wajen azabtar da 'yan ci-rani, har da kashe su, amma babu yadda za a iya tabbatar da ko shi ne wanda Seun ke magana a kai.

'Ya taimake ni'

An bukaci Seun da ya biya dala 500 ta Amurka a matsayin kudin fansa. Kuma dole a saka kudin a wani asusun ajiya na banki a Najeriya. Seun ba shi da kudin, sabili da haka sai ya kira budurwarsa, ya bata umarnin ta sayar da motarsa.

"Motar tsohuwa ce. Sai bayan wata uku ta sayar da ita", in ji Seun. "Ba ta sami masu sayan motar ba".

Abin takaicin shi ne Seun ya yanke hukuncin zuwa Libya ne sabili da ya kasa gyara motar tasa.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Yadda nake sumogar 'yan Najeriya zuwa Turai

Da karshe an biya kudin fansarsa a watan Disamba. Sai Seun ya zaci ya sami 'yancinsa.

Amma lamarin ba haka yake ba, domin an sanar da shi sai ya biya "kudin kofa" na kimanin dala 50 kafin a sake shi. Ga shi ba shi da kudi. Amma wani dan Najeriya mai sayar da biredi a gidan kason ya tausaya masa, kuma ya biya kudin.

"Ya taimaka min kwarai da ya fitar da ni daga wurin nan - mugun wuri ne, mugun wuri ne matuka", in ji Seun.

Seun ya biya mutumin ta hanyar yin aiki a gidan biredinsa na makonni masu yawa a Sabha.

Daga nan ya wuce zuwa birnin Trabulus, amma sai 'yan sandan Libya suka tsare shi. A watan Afrilun da ya gabata ne aka mayar da shi Najeriya.

Yanzu ya koma birnin Legas, amma ba shi da aikin yi, yana hayar wani dan karamin daki ne a wata anguwar marasa galihu. Kuma yana kokarin samo bakin zaren rayuwarsa.

Yana fatar samun kudin sayan wata motar da zai yi tukin tasi da ita, kamar da. Yana fatar komawa wata unguwar wacce tafi wannan domin karamar 'yarsa ta iya ziyartarsa. Yayi nadamar kama hanya zuwa Turai da yayi.

"Hamada wuri ne mai matukar hatsari", in ji shi. "Mutane da yawa sun mutu a kan hanya. Bai kamaci kowa ya bi wannan hanyar ba."

Karin bayani